Babban Daraktan Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC Limited, Bayo Ojulari, ya amince cewa matatun man gwamnati a Najeriya suna tafiya ne da babbar asarar kuɗi, lamarin da ya tilasta wa shugabancinsa dakatar da ayyukansu domin hana ƙarin asara.
Ojulari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a Taron Makamashi na Duniya na Najeriya (Nigeria International Energy Summit) na 2026 da aka gudanar a Abuja. Ya ce fushin ’yan Najeriya ya dace, la’akari da biliyoyin kuɗaɗen da aka kashe a kan matatun man tsawon shekaru.
“Game da matatun man, ’yan Najeriya sun fusata. An kashe kuɗi masu yawa, kuma tsammani ya yi girma ƙwarai. Don haka muna ƙarƙashin matsin lamba mai tsanani,” in ji shi.
Ojulari, wanda ya gina aikinsa a sashen upstream na man fetur, ya ce ya fuskanci ƙalubalen koyon harkar tace mai cikin gaggawa.
“Tushen aikina a upstream ne, don haka na shiga wani yanayi na koyon aiki cikin sauri. Kana da alhaki, dole ka koyi abu da wuri. In ba haka ba, babu mafita,” ya bayyana.
Binciken da aka yi kan ayyukan matatun man ya nuna asarar kuɗi mai tsanani. “Abu na farko da ya fito fili shi ne cewa muna tafiya da babban asara ga Najeriya. Kuɗi kawai muke ɓatawa,” in ji Ojulari. Ya ƙara da cewa yawan amfani da ƙarfin matatun ya tsaya ne a tsakanin kashi 50 zuwa 55 cikin ɗari, duk da ci gaba da samar da danyen mai.
Ya jaddada cewa babu sahihin shirin farfaɗo da matatun. “A wasu lokuta ana iya yin asara a lokacin zuba jari, amma kana da hangen nesa na yadda za a farfaɗo. A nan, wannan hangen nesa bai bayyana ba,” in ji shi. Ya ce babbar shawarar farko da gwamnatinsa ta ɗauka ita ce dakatar da ayyukan domin sake tantancewa.
Ojulari ya kuma nuna raunin ingancin kayayyakin da ake samu daga matatun a matsayin wata matsala. “Danyen man da muke kaiwa Port Harcourt yana fitar da kayayyaki masu matsakaicin inganci. Idan ka tara darajarsu ka kwatanta da abin da ka saka, asara ce tsantsa,” ya bayyana.
Ya amince da cewa akwai matsin lambar siyasa na ci gaba da tafiyar da matatun man, amma ya jaddada cewa riba da ingancin kasuwanci dole ne su zo gaba. “Akwai matsin lamba na siyasa a ci gaba da tace mai. Amma idan ka yi horo fiye da shekaru 35 kana mai da hankali kan kasuwanci da riba, ba za ka iya yin barci da irin wannan yanayi ba,” in ji Ojulari.
