Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gyare-gyaren manufofin Shugaba Bola Tinubu sun hana jihohi 27 faɗawa cikin durƙushewar tattalin arziƙi.
Idris ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi na jama’a a wajen bikin yaye ɗalibai karo na 34 na Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna (FUT Minna).
Ministan ya ce kafin 29 ga Mayu, 2023, ba ƙasa da jihohi 27 ke fama da matsanancin ƙarancin kuɗi har suka kasa biyan albashin ma’aikata da sauran muhimman nauye-nauyen kuɗi. Sai dai ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen juya wannan mummunan yanayi.
Idris ya bayyana cewa rabon kuɗaɗen doka (statutory allocation) da ake bai wa jihohi ya ƙaru sosai, inda ya ce ya ninka fiye da sau uku idan aka kwatanta da yadda yake a baya.
“Rabonnin kuɗaɗen doka da ake bai wa jihohi sun ƙaru ƙwarai, lamarin da ya ba su damar biyan bashin albashi da inganta ayyukan gwamnati,” in ji Idris.
A cewarsa, wannan ci gaban ya ba jihohi damar biyan basussukan albashi, aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da kuma inganta hidimar da ake bai wa al’umma.
Ministan ya jaddada cewa waɗannan nasarori sun samo asali ne daga gyare-gyare na gangan da kuma tsarin jagoranci mai maida hankali na gwamnatin Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa ba za a iya cimma dorewar ci gaban ƙasa ba sai da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen manufofi. A cikin jawabin nasa, Idris ya nuna muhimmancin shigar matasa cikin harkokin ci gaban ƙasa.
Idris ya ƙara da cewa gyare-gyaren suna ƙirƙirar sabbin damammaki ga matasan Najeriya, tare da ba su damar taka rawa mai ma’ana wajen bunƙasar ƙasar.
Ya yi gargaɗin cewa ba tare da waɗannan tsare-tsare ba, Najeriya da ta fuskanci manyan ƙalubalen tattalin arziƙi.
