Manyan kamfanonin masana’antu takwas a Najeriya sun kashe jimillar N1.01 tiriliyan kan makamashi da kayan aiki a cikin watanni tara da suka ƙare a 30 ga Satumba, 2025.
Wannan ya nuna ƙaruwa da kashi 21.1 cikin ɗari idan aka kwatanta da N828.6bn da aka kashe a daidai wannan lokaci a shekarar 2024, kamar yadda bayanan kuɗi na wucin-gadi (unaudited) na kamfanonin suka nuna.
Kuɗin makamashi ya tashi zuwa N195.36bn, wanda ke nuna ƙaruwa da kashi 18.7 cikin ɗari daga N170.51bn a bara, yayin da kuɗin kayan aiki da abubuwan amfani ya haura N811.51bn, ƙaruwa da kashi 21.7 cikin ɗari.
Masana sun ce wannan hauhawar na nuna matsin lambar hauhawar farashi da ke ci gaba da shafar sassan siminti, abinci, giya, gilashi, kiwon lafiya da noma.
BUA Cement ta kashe N113.42bn kan makamashi, ƙaruwa da kashi 11.8 cikin ɗari, yayin da kuɗin abubuwan amfani ya ƙaru da kashi 27 cikin ɗari zuwa N4.44bn. BUA Foods kuma ta kashe N46.45bn kan makamashi, ƙaruwa da kashi 25.3 cikin ɗari, abin da ke nuna tsadar man fetur da wutar lantarki.
International Breweries ta ruwaito amfani da kayan aiki na N260.17bn, ƙaruwa da kashi 23.5 cikin ɗari idan aka kwatanta da 2024. Haka nan Nigerian Breweries ta fuskanci ƙarin kuɗin shigar kaya, inda kayan aiki da abubuwan amfani suka ƙaru da kashi 19.5 cikin ɗari zuwa N486.88bn.
Beta Glass ta ga kuɗin kayan aiki ya ƙaru da kashi 21.8 cikin ɗari zuwa N28.01bn, yayin da kuɗin makamashi ya tashi da kashi 7.5 cikin ɗari zuwa N24.52bn.
Presco Plc ta fuskanci mafi girman tashin farashi, inda kuɗin kayan aiki ya tashi da kashi 178.1 cikin ɗari zuwa N25.03bn, lamarin da ke nuna tsananin matsin farashi a harkar noma.
UAC ta ruwaito kuɗin wutar lantarki da makamashi na N4.87bn, ƙaruwa da kashi 22.9 cikin ɗari, yayin da Fidson Healthcare ta ce kuɗin makamashinta ya tashi da kashi 30.8 cikin ɗari zuwa N3.99bn.
Champion Breweries na daga cikin kaɗan da suka samu sauƙi, inda kuɗin makamashi da ruwa ya ragu kaɗan da kashi 3.3 cikin ɗari.
Masana masana’antu sun danganta hauhawar kuɗaɗen da ƙalubalen tsari. Segun Kuti-George, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masana’antu Ƙanana (NASSI), ya ce kuɗin makamashi na ci gaba da zama babbar matsala duk da wasu matakan gwamnati kamar tarif na Band A.
Ya bayyana cewa manufofin gwamnati sun taimaka wajen hana hauhawar farashin mai fiye da kima, amma ya jaddada cewa dorewar zaman lafiya a farashi na buƙatar faɗaɗa tace man fetur a cikin gida. “Dole ne matatun mai su fara aiki don tallafa wa abin da Dangote ke yi,” in ji shi.
Kuti-George ya ƙara da cewa wutar lantarki ita ce babbar ƙalubale, yana mai nuni da ƙaranci da rashin ingancin rarrabawa. Ya nuna ɗan kyakkyawan fata game da ɗorewar halin da ake ciki, amma ya gargaɗi cewa gyare-gyare a sashen wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci don gasa da bunƙasar masana’antu.
