Wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan ayarin sojoji ta hanyar tukin mota dauke da bama-bamai a yankin Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno a ranar Talata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar wa manema labarai. Rahotanni sun ce jami’ai biyu manya — Manjo da Laftanar — na daga cikin wadanda lamarin ya shafa.
Harin ya auku ne a kan dakarun da ke dawowa daga wani nasarar aikin tsabtace yankin daga ‘yan ta’adda. Wani jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya ce harin ya janyo babbar barna ga kayan aikin soja, ciki har da motocin yaki masu kariya da na sufuri da ake amfani da su a ci gaba da ayyukan.
“Duk wani aiki na soja yana da kalubale, amma mun shawo kansu. Abin takaici, mun rasa sojoji biyar a wannan lamari. Manga (Kwamandan) lafiya lau yake, kuma aikin na ci gaba,” in ji jami’in.
An kwashe gawarwakin sojojin da suka rasu zuwa Maiduguri, yayin da aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa wuraren jinya domin samun kulawar lafiya. Yankin Timbuktu Triangle ya dade yana zama wuri mai hadari sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, inda aka yi kwanton-bauna da hare-hare a baya, ciki har da kama tare da kashe Birgediya Janar Musa Uba.
Harin na baya-bayan nan ya zo ne kwana guda bayan Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas (Operation Hadin Kai) ta sanar da samun manyan nasarori a yankin.
A ranar Litinin, rundunar ta bayyana cewa ta lalata sansanonin ‘yan ta’adda da dama tare da dakile hare-haren jiragen sama marasa matuka (drones) yayin da ake ci gaba da Operation Desert Sanity.
A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce dakarun sun kwato kayayyakin soja da na dabaru da dama daga hannun ‘yan ta’adda, ciki har da na’urorin sadarwa na Baofeng, alburusai, bindigogi, rumbunan mai (POL), kayan jinya, har ma da tutocin Boko Haram/ISWAP.
Ya kara da cewa duk da hare-haren drone da ‘yan ta’adda suka kai, dakarun sun ci gaba da kai farmaki, sun dakile hare-hare da dama, tare da tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya. Ya ce kwarin gwiwar sojoji na nan daram, kuma duk da rashin tabbas a yanayin tsaro, ana ci gaba da sanya ido sosai.
“Babban Hafsan Sojoji ya tabbatar da cewa ayyuka za su ci gaba. Dakarunmu na nan tsayin daka wajen kawar da barazanar ta’addanci, kare fararen hula, da dawo da zaman lafiya mai dorewa a Arewa Maso Gabas,” in ji Laftanar Kanal Uba.

