Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce an yi wa kalamansa rashin fahimta game da rawar da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya taka a rikicin Boko Haram.
Jonathan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yada labarai, Ikechukwu Eze, ya fitar.
A yayin wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da littafin tsohon babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS), Lucky Irabor, a Abuja, Jonathan ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa, kungiyar Boko Haram ta taba zaben Buhari a matsayin mai shiga tsakani.
Wannan magana tasa ta jawo cece-kuce, musamman daga jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC).
Sai dai, a cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, Jonathan ya bayyana cewa kalamansa “an fassara su ba daidai ba.”
Sanarwar ta ce: “A kowane lokaci, Dr. Jonathan bai taɓa nuna ko da alamar cewa tsohon shugaban ƙasa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba, kuma bai taɓa cewa yana goyon bayan ƙungiyar a kowace irin hanya ba.”
A cewar sanarwar, bayanin da Jonathan ya yi game da ta’addanci “yana nufin bayyana dabarun yaudara da amfani da dabaru na siyasa da kungiyar Boko Haram ta yi a farkon shekarun ta.”
Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani rahoto da ya rikita ma’anar kalaman Jonathan, tana mai jaddada cewa tsohon shugaban ƙasa “yana nan daram wajen goyon bayan zaman lafiya, haɗin kan ƙasa, da kuma ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.”







