Matatar Mai ta Dangote ta dakatar da sayar da man fetur da Naira, mataki da ya tayar da hankalin ‘yan kasuwar mai tare da haifar da fargabar ƙarin matsin lamba kan farashin famfo da kuma kasuwar musayar kuɗi.
A cikin wani saƙo ta imel da aka aika wa abokan ciniki da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin Juma’a, matatar ta sanar da cewa dakatarwar za ta fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.
An bayyana cewa dalilin wannan yanke shawara shi ne ƙarewar rabon danyen mai da ake samun sa da Naira.
Sanarwar, wacce sashen harkokin kasuwanci na Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ya fitar da take “Suspension of DPRP PMS Naira Sales Effective 28th September 2025”, ta shawarci abokan ciniki da ke da mu’amalar Naira da ba a kammala ba su nemi a maido musu da kuɗinsu.
A wani ɓangare na sanarwar an ce:
“Muna sanar da ku cewa Dangote Petroleum Refinery & Petrochemicals ta riga ta sayar da kayayyakin mai fiye da rabon danyen mai da ake samu da Naira, saboda haka ba za mu iya ci gaba da sayar da PMS da Naira ba.
“Ku sani cewa wannan dakatarwar za ta fara aiki daga Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.
“Za mu bayar da ƙarin bayani kan dawo da sayarwa idan aka warware lamarin. Duk abokan ciniki da ke da mu’amalar PMS da Naira kuma suke son a maido musu da kuɗin su, su rubuta buƙata domin a fara aiwatar da maidowa.”
Wannan ba shi ne karon farko da matatar ta dakatar da sayar da kayayyaki da Naira ba. A watan Maris 2025, ta taɓa dakatar da irin wannan mu’amala, inda ta ce ƙarancin rabon danyen mai da ake samu da Naira ne ya jawo.
Wannan matakin na baya ya haifar da fargabar yiwuwar “dollarisation” na kasuwancin mai, tare da tura farashin fetur a famfo kusan Naira 1,000 a kowace lita.
