Trends

Gwamnatin Tinubu ta fi kowace Gwamnatin Soja Muni a Tarihin Najeriya – El-Rufai

Mallam Nasir El-Rufai Tsohon gwamnan Kaduna

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fi kowace gwamnatin soja da Najeriya ta taɓa fuskanta muni.

El-Rufai ya yi wannan magana ne a lokacin da ya karɓi bakuncin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a ƙarshen mako. Atiku ya kai masa ziyara ta nuna goyon baya bayan harin da aka kai lokacin kaddamar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kaduna, inda ‘yan daba suka tarwatsa taron.

A cewar El-Rufai, gwamnatin Tinubu tana tafiya ne a kan hanyar kama-karya, inda ya kwatanta shugaban Najeriya da shugaban Kamaru, Paul Biya, wanda ya rike mulki tun daga shekarar 1982.

“Gaskiya ranka ya daɗe, wannan abin kunya ne. Mutane sun shafe shekaru suna ikirarin kishin dimokuraɗiyya da NADECO, suna cewa suna fafutukar gaskiyar tsarin tarayya, amma duk shirme ne, karya ce. Domin wannan gwamnati ta Tinubu tana ƙoƙarin tattara duka iko a tsakiya maimakon ta sauke shi zuwa ƙananan matakai,” in ji shi.

Ya ce wannan hali na nuna cewa Najeriya na fuskantar babbar barazana a tarihi, yana mai gargadin cewa idan ba a kawar da wannan gwamnati a shekarar 2027 ba, Tinubu zai nemi zama kamar Paul Biya.

El-Rufai ya kuma yaba da rawar da Atiku ya taka a gwagwarmayar dimokuraɗiyya a baya, yana mai cewa jama’a suna sa ran zai jagoranci kawancen adawa.

“Kai (Atiku Abubakar) shugaba ne, ka yi wannan gwagwarmaya a baya, ka fafata da sojoji, kana da kwarewa a mulkin dimokuraɗiyya. A lokacin da kai da Obasanjo kuka shugabanci wannan ƙasa, babu wanda aka tsananta masa saboda ra’ayin siyasa daban. Ko Buhari ma, da tarihin soja a bayansa, bai taɓa yin hakan ba. Amma yau muna fuskantar fararen hula, amma sun fi kowace gwamnatin soja muni,” in ji El-Rufai.

Ya ƙara da cewa: “Kiran ka na cewa mu haɗa kai ya zo a kan gaba. Mutanen Najeriya sun gama yanke shawara cewa dole APC ta bar mulki. Suna jiran a kore ta. Dole mu samar da jagoranci da haɗin kai kamar yadda muka tattauna, kuma da jagorancinka da hikimarka, tabbas za mu isa ga ƙasar da muke mafarki.”

A nasa jawabin, Atiku ya yaba wa El-Rufai, inda ya jaddada cewa dole ne shugabannin adawa su kasance masu daidaito da mayar da hankali wajen tabbatar da cewa Tinubu ya sha kaye a 2027.

“Ina sane cewa kai ba mutum bane mai tsoron fuskantar irin wannan yanayi. Wannan shi ya sa ya zama dole mu haɗa kai domin mu tabbatar da cewa, ɗaya, hakan bai sake faruwa ba a wannan gwamnati; sannan, biyu, kamar yadda ka fada, mu kore su a 2027—ba ta kowace hanya ba sai ta akwatin zaɓe,” in ji Atiku.