Trends

Shugaban PRNigeria ya Maka NIPSS Kotu, ya Nemi Diyya na Naira Biliyan Daya

Yusha'a Shaibu Shugaban PRNigeria

Shugaban PRNigeria da Image Merchants Ltd, Malam Yushau A. Shuaib, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya dake Abuja kan janye shi daga Senior Executive Course (SEC) 47 na Cibiyar Nazarin Manufofi da Tsare-tsare (NIPSS), Kuru, jihar Filato.

A cikin ƙarar da aka yi wa alamar FHC/ABJ/CS/1329/2025, Shuaib ya nemi a biya shi diyya ta Naira biliyan ɗaya (₦1bn) a matsayin biyan kuɗaɗen raɗaɗin rai da ɓata suna, tare da ƙarin Naira miliyan ɗari (₦100m) a matsayin kuɗin shari’a, bayan ya aike da wasiƙar gargaɗi ga Darakta Janar na NIPSS, Farfesa Ayo Omotayo, tun ranar 16 ga Yuni, 2025, amma ba a ɗauki mataki ba.

Lauyansa, babban lauya (SAN) Yunus Abdulsalam, ne ya shigar da ƙarar a madadinsa, inda yake neman kotu ta soke janye shi daga SEC 47 tare da dawo da shi cikin cikakken ‘yanci da fa’idodi.

Shuaib ya kuma nemi kotu ta bayar da umarnin hana NIPSS, jami’anta ko wakilansa ci gaba da tsangwama, barazana ko cin zarafi ta yanar gizo.

A cikin buƙatun ƙarar, Shuaib ya bayyana cewa wani labari da PRNigeria ta wallafa ba za a iya ɗora masa laifi ba, domin ba shi ne ya rubuta ko ya amince da shi ba. Haka kuma ya kalubalanci yadda aka samu damar shiga da amfani da imel ɗinsa ba tare da izini ba, yana mai cewa hakan ya karya haƙƙinsa na sirri da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a sashe na 37.

Ya ce ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa saboda ra’ayoyin ƙwararru da aka wallafa ya sabawa haƙƙinsa na faɗin albarkacin baki da doka ta tanada a sashe na 39(1). Haka kuma ware shi daga tattaunawa da takwarorinsa da kuma cire shi daga dandalin hukuma, a cewarsa, ya zama wata irin cin zarafi, barazana ta yanar gizo da kuma ware shi da gangan.

Ya ƙara da cewa ƙin ba shi damar shiga yawon karatu na ƙasashen waje duk da cewa ya biya kuɗin shiga kwas ɗin har Naira miliyan 18.3, ya zama wariya da karya yarjejeniya.

Haka zalika, ya soki dakatar da shi bisa wani zargi na “externalisation of the subject” ba tare da an bashi damar kare kansa ba, inda kuma ya ce kama masa daftarin sharhi mai taken “Understanding the ‘Blue’ in the Blue Economy” ya sabawa haƙƙinsa na samun adalci da kundin tsarin mulki ya tanada a sashe na 36(1).

A ƙarshe, Shuaib ya nemi kotu ta dawo da shi cikin SEC 47 da cikakken ‘yanci da fa’idodi, ta bayyana cewa NIPSS ba ta da hurumin ladabtar da shi saboda wani abu da wata jarida mai zaman kanta ta wallafa, ta tabbatar cewa shiga imel ɗinsa ba bisa izini ba ya sabawa doka, tare da bayyana cewa janye shi daga kwas ɗin ba bisa ƙa’ida ba ne, zalunci ne kuma wariya ce.

Har yanzu dai ba a saka ranar sauraron shari’ar ba.