Trends

Majalisar Dinkin Duniya: Shettima Zai Wakilci Najeriya Karo na 80 a New York

Kashim Shettima a filin jirgin jihar kogi. Photo credit The Guardian

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 (UNGA), wanda zai gudana daga Litinin, 22 ga Satumba zuwa Lahadi, 28 ga Satumba, 2025, a birnin New York, Amurka.

Wannan umarni ya fito ne daga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya na ƙasa a ranar Laraba, 24 ga Satumba – wani muhimmin lokaci da ake sa ran Najeriya za ta fayyace manufofinta a idon duniya.

Haka kuma, a wannan rana ɗaya, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai halarci taron musamman kan sauyin yanayi da aka shirya wa shugabannin ƙasashe, wanda Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya jagoranta. Ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudaden da ta ƙudura (NDCs) ƙarƙashin yarjejeniyar Paris.

Wani muhimmin taro da Shettima zai halarta shi ne zagaye na musamman kan gidaje masu araha da nagarta, wanda Shugaban Ƙasar Kenya zai jagoranta. Wannan zai kasance a lokaci guda da wasu tattaunawa na bangarori daban-daban da kuma tarukan haɗin gwiwa.

Masu lura da lamurra suna hasashen Shettima zai yi amfani da wannan dandalin wajen fayyace matsayar Najeriya kan sauyin yanayi, farfaɗo da tattalin arziki, samar da gidaje da kuma tsaro – musamman duba da ƙalubalen da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta, irin su sauyin yanayi, rikice-rikicen yankuna, da durƙushewar tattalin arziki.

Bayan kammala taron a New York, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai zarce zuwa Frankfurt, Jamus, domin ganawa da jami’an Deutsche Bank, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar kasuwanci da zuba jari.

Shugabancin Najeriya na da burin amfani da wannan taron UNGA wajen jawo hannun jari daga ƙasashen waje, samun kuɗaɗen sauyin yanayi, da ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni irin su makamashi da ababen more rayuwa.