Trends

Yajin Aiki: Na Amince da a Biya Duk Bukatun Likitocin FCT – Wike

Nyesom Wike Minista Birnin Tarayya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya amince da dukkan bukatun likitocin horaswa da ke kan yajin aiki tun daga 15 ga Satumba, 2025, saboda bashin albashi da ba a biya ba.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da aikin titin Northern Parkway daga Ring Road II zuwa Ring Road III a Shehu Yar’Adua Way, kusa da Life Camp, Abuja.

Ministan ya yaba wa likitocin bisa janye yajin aikin da suka fara, yana mai cewa hakan ya dace da jin dadin marasa lafiya da kuma al’ummar FCT gaba daya.

Ya ce dukkan takardun da suka kunshi bukatun likitocin da ke kan teburi na ofishinsa, ya sanya musu hannu. Haka kuma ya umarci mukaddashin Shugaban Ma’aikata na FCT tare da Mai Baiwa Shawara na Musamman kan Harkokin Gudanarwa, Samuel Atang, da su aiwatar da su yadda ya dace.

“Ina yaba wa likitocin horaswa bisa janye yajin aikin. Hukumar tana farin ciki da fahimtar da suka nuna. Na sanya hannu kan dukkan bukatun likitocin da ke kan teburi na yau,” in ji Wike.

Likitocin sun fara yajin aikin ne a makon da ya gabata domin tilasta gwamnati ta biya bukatunsu bayan watanni na tattaunawa ba tare da sakamako ba.

Daga cikin bukatun likitocin akwai:

Biyan bashin albashi daga wata daya zuwa watanni shida ga mambobin da aka dauka aiki tun daga 2023,

Daukar sababbin ma’aikata cikin gaggawa,

Biyan kudaden horo na Medical Residency Training Fund na shekarar 2025,

Biyan bashin da ya taso daga karin kashi 25/35 cikin 100 na tsarin albashin likitoci (CONMESS),

Bayar da takamaiman lokacin kammala tsarin skipping da conversion ga dukkan mambobi,

Da kuma biyan dukkan bashin da ya taru a baya.