Trends

Bazan kasance Ministan FCT ba a cikin shekara biyu masu zuwa – Wike

Nyesom Wike Ministan Babban Birnin Tarayya

Tsohon gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Juma’a ya bayyana yiwuwar cewa ba zai kasance Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT) ba cikin shekara biyu masu zuwa.

Wike ya yi wannan karin haske ne yayin kaddamar da aikin gina titin Northern Parkway daga Ring Road II zuwa Ring Road III da ke Abuja.

Yayin jawabi game da wa’adin watanni 30 da aka bai wa kamfanin da ke gudanar da aikin, Wike ya ce:

“Watanni 30 kusan shekaru biyu ne, kuma a lokacin zan riga na bar ofis. Don haka ya kamata a fara aikin yadda zan halarci kaddamarwarsa kafin in tafi. Kamar yadda na fada jiya, Shugaban kasa ya bayyana a fili cewa a karkashin shirin Renewed Hope, dole Abuja ta zama kamar sauran manyan biranen duniya.”

Ya kara da cewa ingantaccen tsarin hanyoyi shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa, yana mai bayyana yadda hasken tituna ke kara kyawun gari musamman idan aka kalli birni daga sama da daddare.

“Idan duk wurare suna dauke da haske, sai ka ce gari ne mai kyau. Amma babu hanyoyi, to zai yi wahala ka ce birnin na cikin jerin manyan birane na duniya. Ina ganin a karkashin Renewed Hope Agenda na Shugaban kasa, muna canza alkibla domin tabbatar da cewa Abuja ta yi gogayya da sauran biranen duniya,” in ji shi.

Wike ya kuma tabbatar da kudirin gwamnati na sauya fasalin Abuja zuwa birni na zamani, wanda zai dace da tsare-tsaren ci gaban Shugaba Bola Ahmed Tinubu.