Kungiyar Obidient ta bukaci tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya mara baya ga Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, maimakon ya tsaya takara a kansa yayin shirye-shiryen zaben 2027.
Wannan na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da Obi da Jonathan suka yi a Abuja ranar Alhamis, a yayin da ake ƙara tattaunawa kan yiwuwar hadewar jam’iyyun adawa kafin 2027.
Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanan ganawar ba, Obi ya wallafa hotunansu a shafinsa na X, inda ya bayyana Jonathan a matsayin “babban ɗan uwa, dattijo kuma jagora,” tare da jaddada cewa tattaunawarsu ta shafi halin da ƙasar ke ciki.
Sai dai jagororin Obidient Movement sun bayyana matsayinsu kai tsaye, suna mai cewa Jonathan ya kamata ya ja baya ya ba Obi dama, don adalci da ci gaban ƙasa.
Shugaban ƙasa na kungiyar, Dr. Yunusa Tanko, ya shaida wa manema labarai cewa duk da cewa mutanen biyu shugabanni ne masu daraja, Obi ne har yanzu zabin dubban ’yan Najeriya masu neman sabon shugabanci.
“Tuni suna da alaka ta abota tun tsawon lokaci. Ganawar da suka yi wata dama ce ta tattauna yadda za a ceto Najeriya. Amma a gare mu a Obidient Movement, zai yi kyau idan Jonathan ya ci gaba da kasancewa dattijo mai mutunci kamar yadda aka san shi. Ya riga ya yi nasu lokacin a matsayin shugaban ƙasa, yana da mutunci, yanzu lokaci ne na goyon bayan ɗan uwansa,” in ji Tanko.
Ya tunatar da cewa Obi ya kasance cikin tawagar gudanar da tattalin arzikin gwamnatin Jonathan a lokacin mulkinsa, yana mai jaddada cewa yanzu lokaci ne na tsohon shugaban ƙasa ya biya wannan alfarma ta hanyar mara masa baya a burinsa na 2027.
Tanko ya kara da cewa wasu ’yan siyasa na shirin amfani da Jonathan wajen rage karfin Obi, amma kungiyar Obidient ba za ta bari hakan ya yi nasara ba.
“Mun san irin waɗannan shirye-shirye, amma muna da yakinin ba za su yi nasara ba. ’Yan Najeriya da dama na ganin shugaban ƙasa na gaba ya fito daga Kudu, kuma don adalci, yankin Kudu maso Gabas ya dace ya samu dama. Peter Obi shi ne zabin da ya dace,” in ji shi.
Majiyoyi daga bangarorin biyu sun tabbatar da cewa Jonathan da Obi sun yi ganawa a kalla sau uku tun daga lokacin Easter domin tattauna yiwuwar haɗin gwiwa.
Babban abin tattaunawa dai shi ne wanda zai ja baya don ɗayan ya tsaya takara a matsayin ɗan takarar haɗin gwiwa.
Dukkaninsu sun amince cewa suna da tushen siyasa iri ɗaya a Kudancin Najeriya da kuma tsakiyar ƙasa (Middle Belt), lamarin da ke tayar da fargabar cewa idan kowannensu ya tsaya dabam, hakan zai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar samun saukin sake lashe zabe.
Yayin da jagororin PDP da ADC ke neman Jonathan saboda suna ganin yana da ƙarin karɓuwa a Arewacin ƙasar, bangaren Obi na jaddada cewa karfin da ya samu a 2023 da kuma tasirin Obidient Movement na sa shi zama zabin da ya fi dacewa.
