Trends

Babban Layin Wutar Lantarki na Ƙasa ya Sake Faduwa

Grid ɗin wutar lantarki na ƙasa ya samu rugujewa a ranar Laraba, lamarin da ya jefa ƙasar cikin duhu baki ɗaya.

Bisa bayanan da Independent System Operator (ISO) ta fitar, an tabbatar da cewa yawan samar da wutar lantarki ya faɗi daga 2,917.83 megawatts (MW) zuwa kawai 1.5MW tsakanin ƙarfe 11:00 na safe zuwa 12:00 na rana, abin da ya tabbatar da faduwar grid ɗin gaba ɗaya.

Kamfanin Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ya fitar da sanarwa ga kwastomominsa, inda ya danganta katsewar wuta a yankunan da yake rufewa da rushewar grid ɗin na ƙasa, wanda ya faru a kusan ƙarfe 11:23 na safe.

A cikin sanarwar, kamfanin ya ce:
“Muna sanar da kwastomominmu cewa rashin wutar lantarki da ake fuskanta yanzu ya samo asali ne daga rushewar grid ɗin ƙasa da ya faru da misalin ƙarfe 11:23 na safe, wanda ya shafi rabon wuta a dukkan yankinmu.”

Kamfanin ya ƙara da cewa yana cikin tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa domin a dawo da wutar lantarki da wuri bayan da aka daidaita grid ɗin.

“Muna yaba wa kwastomominmu bisa haƙuri da fahimtar da suke nunawa a wannan lokaci,” in ji AEDC.