Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin aikata laifukan karya doka ta jam’iyya da kuma kasa biyan hakkokin kudi da jam’iyyar ke bukata.
Shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Kano ranar Asabar. Ya ce matakin ya biyo bayan matsanancin suka da Jibrin ya rika yi wa jam’iyyar da shugabanninta a kafafen watsa labarai.
Korarren ɗan majalisar ya fito da wannan hukunci kwanaki kaɗan bayan ya kai ziyara ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, abin da ya jawo cece-kuce a siyasar jihar.
Kafin sanarwar korar, Jibrin ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne idan ya bar jam’iyyar, inda ya ƙara da cewa:
“Na isa shekaru da zan iya ɗaukar matsaya ta kaina, in bi abin da na ga ya dace da ni a siyasa,” in ji shi.
