Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa yana cikin cikakken shiri tare da shugabannin adawa domin ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bar ofis ta hanyar dimokuraɗiyya da doka.
Tambuwal ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Juma’a.
“Ina cikin wani tsari — ta hanyar dimokuraɗiyya da doka — wanda a ƙarshen sa, da taimakon Allah da kuma Najeriya, wannan gwamnati za ta bar ofis,” in ji shi.
Ya ce bai yarda da zargin cewa ƙawancen jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya samo asali ne daga Arewa kawai ba.
“Shin Peter Obi ɗan Arewa ne? Shin Aregbesola ba ɗan Osun ba ne? To, me kake gaya min? Su dukkansu suna cikin wannan ƙawance. Wannan ƙawancen ya haɗa al’ummar Najeriya baki ɗaya, ba na Arewa kawai ba,” in ji shi.
Sanatan ya jaddada cewa dole sauyin mulki ya kasance cikin tsarin kundin tsarin mulki da kuma dimokuraɗiyya.
“Ba wani abu bane da aka dasa cikin doka cewa Tinubu ba zai iya faduwa a 2027 ba. Duk wani yunƙuri da ake yi na nuna cewa ba za a iya kayar da shi ba, maganganu ne na banza. Ana iya kayar da shi, kuma na yi imani da haka. Ni da sauran shugabannin ƙawance muna aiki a kai domin amfanin ƙasar nan, ba don Tinubu ko son rai ba, sai don irin yadda yake tafiyar da ƙasar,” in ji Tambuwal.
Ya kuma ce Shugaba Tinubu ba zai iya tsayawa ga ƙarfin haɗin kan jam’iyyun adawa da manyan ’yan siyasa irinsu tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso ba.
“Zai fi sauƙi idan ’yan adawa suka haɗa kai wajen kayar da Tinubu. Amma idan Tinubu, Jonathan, Atiku, Obi da Kwankwaso suka fito dabam-dabam a zabe guda, hakan zai zama hanya mai sauƙi ga Tinubu. Idan aka samu haɗin kai, abubuwa za su sauya kuma jama’a za su kada kuri’unsu ta wani sabon salo,” ya ƙara da cewa.
Da aka tambaye shi kan wanda yake so ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027, Tambuwal ya ce:
“Idan suka fito da yardar kansu, zan dawo na bayyana wanda zan goyi baya,” in ji shi.
