Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Tarayya ta Gargadi Jihohi 14

Yadda Ambaliyar ruwa ya mamaye gidaje photo credit The Guardian

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi cewa jihohi 14 na Najeriya na iya fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama mai yawa da ake sa ran sauka daga ranar 4 zuwa 8 ga Satumba, 2025.

Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Farkon Gargaɗin Ambaliyar Ruwa ta Ƙasa karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Usman Abdullahi Bokani, Daraktan Sashen Kula da Ambaliyar Ruwa, Fashewar Ƙasa da Yankin Teku ya sanya wa hannu.

Hukumar ta yi gargaɗi cewa wurare 43 a faɗin ƙasar na iya fuskantar ambaliya a wannan lokaci, lamarin da ke ƙara tsananta sakamakon sauyin yanayi da kuma rashin isassun magudanan ruwa.

Jihohi da wuraren da abin ya shafa sun haɗa da:

Ebonyi: Afikpo

Cross River: Edor, Ikom, Itigidi, Akpap

Kano: Gwarzo, Karaye

Zamfara: Anka, Gummi, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi, Bukkuyum

Taraba: Dampar, Duchi, Garkowa, Gassol, Gembu, Gun Gun Bodel, Kambari, Mayo Ranewo, Mutum Biyu, Bandawa, Ngaruwa

Abia: Eziama, Umuahia

Yobe: Geidam, Kanama, Potiskum

Plateau: Langtang, Shendam, Wase

Borno: Ngala

Imo: Okigwe, Otoko

Niger: Sarki Pawa

Sokoto: Sokoto, Wamakko, Isa, Shagari, Makira

Kaduna: Kafanchan

Akwa Ibom: Oron

Matsalar Muhalli a Lagos

A halin da ake ciki kuma, Gwamnatin Jihar Lagos ta bayyana damuwa kan yiwuwar afkuwar rikici na muhalli da zamantakewa a Lagos Lagoon.

Kwamishinan Harkokin Kula da Gabar Ruwa, Dayo Alebiosu, ya shaida wa manema labarai a Ikeja cewa tafkin yana fuskantar barazanar rushewa muddin ba a ɗauki matakin gaggawa ba.

Wannan gargadi na zuwa ne kafin taron farko na waterfront summit da za a gudanar a Lagos ranar 11 ga Satumba, mai taken “Pressure on the Lagoon: The Lagos Experience”. Taron zai haɗa kwararru fiye da 500 don tattauna batun faduwar gabar ruwa da hanyoyin magance matsalar.

Alebiosu ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta riga ta share kauyen Idotun da ke Ibeju-Lekki, inda ta rusa gidaje da ta tilasta mazauna su bar wurin – matsala da ake fuskanta a wasu sassan kasar Ghana ma.

Tallafin Kuɗi daga Kasar Sin

Haka kuma, Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Kasafin Kuɗi, Abubakar Bagudu, ya rattaba hannu kan yarjejeniya da Jakadan Sin a Najeriya, Yu Dunhai, a Abuja domin samar da tallafin kuɗi ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa.

Bagudu ya bayyana wannan mataki a matsayin lokaci mai dacewa, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da tallafin cikin gaskiya da kulawa tare da hanyar sa ido ta haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ofishin jakadancin Sin.

A nasa jawabin, Jakada Dunhai ya nuna alhini tare da nuna cewa kasashen biyu sun fuskanci mummunar ambaliya a baya-bayan nan, inda ya jaddada kudirin Beijing na ci gaba da haɗin kai a fannin kare lafiyar al’umma da murmurewa daga bala’o’i.