Gwamnatin Gombe ta Mai da Jewel Suites Ofisoshin Sarakuna

Inuwa Yahaya Gwamnan Jihar Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe, ta hannun Hukumar Cigaban Ayyukan Hada-Hadar Jihohi (GSJPDA), ta fara mayar da Jewel Suites da ke Gombe zuwa ofisoshi ga sarakuna da dagatai 14 na jihar.

Daraktan Hukumar, Mahmoud Yusuf, ya shaida wa manema labarai a Gombe cewa aikin ya kai kashi 70 cikin 100 zuwa yanzu.

Ya ce wannan shiri zai samar wa sarakunan gargajiya da wurin aiki na zamani mai kyau da natsuwa a duk lokacin da suke ziyara a babban birnin jihar.

Yusuf ya kuma bayyana wasu muhimman ayyukan da hukumar ta kammala, ciki har da gina rumfunan kasuwa 260 a Kaltungo, da shaguna 66 tare da gyaran muhalli a Funakaye, sake ginawa da gyaran fadodin dagatai guda biyu, da kuma gyaran fadar Sarkin Nafada.

Ya ƙara da cewa karamar hukumar Akko ta amfana da ayyukan hukumar, ciki har da sanya sabbin fitilun titi da kuma sake gina tsohuwar sakatariyar karamar hukumar.

Daraktan ya jaddada cewa hukumar GSJPDA, wadda aka kafa a shekarar 2020, ta riga ta cimma fiye da kashi 80 cikin 100 na aikinta, inda ya bukaci gwamnati masu zuwa su ci gaba da gina kan wannan gado.

“Dukkan ayyukanmu muna aiwatar da su ne bisa bukatun kananan hukumomi, kuma muna tabbatar da cewa sun dace da bukatun al’umma,” in ji shi.