Wani mummunan lamari ya tayar da jijiyoyin wuya a Mabushi, Abuja, a ranar Laraba, bayan wani taron jama’a ya banka wa wasu ‘yan agbero uku wuta bisa zargin cewa sun haddasa mummunan hatsari da ya kashe wani mutum tare da matarsa da ɗansu, lokacin da suka yi ƙoƙarin kwace sitiyarin motar iyalin.
Bayanan sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kan gadar Mabushi, lokacin da ake zargin ‘yan agberon – waɗanda ake danganta da Abuja Municipal Area Council (AMAC) – suka yi ƙoƙarin kwace sitiyarin mota daga hannun direban iyalin yayin da suke neman tilasta masa biyan kuɗi. Wannan ya jawo hatsarin mota mai muni wanda ya yi ajalin dukan iyalin nan take.
A wani bidiyo da SaharaReporters ta samu, an ga mutanen uku a kwance ƙasa kafin wani da ba a san ko wanene ba ya zuba musu man fetur ya kuma banka musu wuta.
A cikin bidiyon, wani murya ta na roƙon Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da ya shiga lamarin, tare da dakatar da ‘yan AMAC agbero daga aiki a Abuja, yana mai cewa ana ta samun matsaloli iri ɗaya na cin zarafi da tashin hankali daga gare su.
Wani ganau ya shaida cewa:
“Ga abin da ‘yan agbero na AMAC suka haddasa a nan Abuja. Su na cutarwa sosai. Lokaci ya yi da za a ɗauki mataki. Iyali gaba ɗaya sun mutu saboda agbero. Ka ga yadda suka bi wannan mutumin, suka shiga cikin motarsa, suka yi masa ƙwace sitiyari. Mutumin ya mutu, matarsa ta mutu, ɗansa ma ya mutu. FCT Minister ya kamata ya ɗauki mataki. ‘Yan agbero na AMAC dole su bar Abuja.”
Source: Sahara Reporters

