Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya rusa majalisar zartarwar jiharsa.
Sai dai gwamnan ya ci gaba da barin Sakataren Gwamnatin Jiha, Babban Jami’in Fada (Chief of Staff), Mataimakin Babban Jami’in Fada (Deputy Chief of Staff) da kuma wasu manyan jami’an gwamnati a mukamansu.
A cewar mai magana da yawun gwamnan, Bologi Ibrahim, rushewar majalisar ta zartarwa an sanar da ita ne a taron majalisar zartarwa da aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnati da ke Minna, a ranar Litinin.
Gwamna Bago ya bayyana godiyarsa ga mambobin majalisar bisa irin hidimar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da za su gudanar nan gaba.

