Gwamna Hope Uzodinma ya sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa naira dubu 104 a jihar Imo da ke Kudancin Najeriya.
Gwamnan ya tabbbatar da ƙarin mafi ƙarancin albashin a daren jiya, lokacin da yake ganawa da ƙungiyoyin ƙwadago a fadar gwamnati da ke Owerri.
Kamfanin dillancin labarai a ƙasar ya rawaito cewa an ƙara mafi ƙarancin albashin ne daga naira dubu 76 zuwa dubu 106.
Baya ga haka gwamnan Imo Hope Uzodinma ya ƙara mafi ƙarancin albashin likitoci zuwa dubu 503 daga naira 215 a jihar tare da ƙara na malaman manyan makarantun jihar daga naira dubu 119 zuwa naira dubu 222.
Uzodinma ya ce ƴan jihar Imo suna fuskantar ƙalubale iri-iri, kama daga annobar Covid19 da matsin tattalin arziƙi da wahalar da ƙudirorin gwamnati ya haddasa da ma batun cire tallafin man fetur
Gwamnan ya ce a shekarar 2020 suna karbar naira biliyan 5 zuwa biliyan 7 a matsayin kason gwamnatin jihar daga tarayya, amma a yanzu suna karɓar kuɗin da ya kai biliyan 14.
Baya ga haka gwamnan ya ce za a fara biyan kaso na ƙarshe na garatuti da ya kai biliyan 16 a yau 27 ga watan Agusta.
Da yake tsokaci shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Mr Uchechigemezu Nwigwe ya kwatanta ƙarin mafi ƙarancin albashin da gwamnan ya yi a matsyain wata gagarumar nasara ga dukkanin ma’aikatan jihar.
