Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ba za ta bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tikitin kai-tsaye na neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba, duk da cewa ya riga ya samu amincewar jam’iyyar a matsayin ɗan takarar ta.
Suleiman Argungu, Sakatare na Ƙasa mai kula da Ƙungiyoyi (National Organising Secretary), ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa.
A cewar rahoton da bayyana ga maneman labarai, sauran mambobin jam’iyyar ma suna da damar sayen fom ɗin tsayawa takara domin shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Argungu ya bayyana cewa, ko da yake kwamitin riko na jam’iyyar (NWC), gwamnonin jihohi, da kuma kowane ɗaya daga cikin shiyyoyi shida na ƙasar sun nuna goyon baya ga Tinubu, hakan bai rufe ƙofa ga masu sha’awar tsayawa takara ba.
Ya ƙara da cewa, jam’iyyar za ta fitar da jadawalin ta a lokacin da ya dace, domin bai wa masu sha’awar neman kujerar shugaban ƙasa damar mika fom ɗinsu a hukumance.
“Zabin jam’iyyar kenan, kuma mu a matsayin NWC mun riga mun amince da Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na gaba a karkashin APC. Haka kuma sauran sassan jam’iyyar sun yi hakan.
Gwamnoni a jihohi sun yi hakan. Haka ma aka yi a shiyyoyi shida na ƙasar. Amma wannan ba yana nufin cewa an rufe ƙofa ba.
Ma’ana, idan lokacin ya yi, za mu fitar da jadawalinmu, domin duk wanda ke sha’awar neman shugabancin ƙasa a karkashin jam’iyyar APC ba za a hana shi damar sayen fom ɗin tsayawa takara ba,” in ji Argungu.
