Almundahana: Baltasar ya Samu Hukuncin Daurin Shekaru 8

Kotu a Ƙasar Equatorial Guinea ta yanke wa tsohon babban jami’in gwamnati, Baltasar Ebang Engonga, hukuncin daurin shekaru takwas a gidan yari kan laifin almundahanar kuɗi.

Hukuncin ya zo ne watanni bayan Engonga ya shiga tsakiyar rikicin duniya sakamakon bayyanar bidiyon batsa da suka bazu a kafafen sada zumunta.

Kotun lardin Bioko ta tabbatar da Engonga da laifin karkatar da kuɗaɗen jama’a ta hanyar ƙirƙirar kuɗin tafiyar aiki da ya mayar da na kansa. Wannan hukunci ya samu tabbaci daga Hilario Mitogo, Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Koli, wanda ya bayyana wa manema labarai.

Engonga, wanda ake kuma kira da “Bello,” tsohon Darakta Janar ne na Hukumar Kasa ta Binciken Kuɗi. An yi masa shari’a tare da wasu jami’ai biyar da ake tuhuma da karkatar da ɗaruruwan dubban dalolin gwamnati.

Engonga ya fara jawo hankalin duniya ne a watan Nuwamba 2024, lokacin da jerin bidiyoyin batsa da suka shafe shi suka bayyana a shafukan sada zumunta wasu daga cikinsu ma an ce a ofishin ma’aikatar kuɗi aka yi ɗaukar su yayin da yake tsare yana jiran shari’a.