Dangantaka tsakanin fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya, Ademola Lookman, da kungiyar Atalanta ta shiga wani sabon hali. An cire shi daga cikin jerin ‘yan wasa 23 da za su buga wasan farko na kakar Serie A da Pisa, lamarin da ya biyo bayan rikicin canja shekarsa da ya jefa makomarsa cikin duhu.
Kimanin watanni uku kacal da suka gabata, Lookman mai shekaru 27 ya zama gwarzon kungiyar bayan zura kwallaye uku (hat trick) da suka bai wa Atalanta kambun farko na Turai a tarihi.
Amma yanzu ya koma yin atisaye shi kaɗai, ba tare da tawaga ba. Rikicin ya fara ne tun lokacin da Inter Milan ta bayar da tayin euro miliyan 45 a farkon watan Agusta, amma Atalanta ta ƙi karɓa, tana nacewa kan kimar euro miliyan 50.
Lookman ya nuna bacin ransa, inda ya zargi kulob ɗin da karya alƙawari da kuma rashin adalci. Daga bisani ya ɗauki hutu na makonni biyu ba tare da izini ba daga horon bazara, sannan ya miƙa buƙatar sauya sheƙa a hukumance domin matsa lamba kan tafiyarsa zuwa Inter.
Sai dai daga ƙarshe Inter ta ja da baya saboda rashin iya biyan kuɗin da Atalanta ke nema. Lookman ya koma Bergamo, amma maimakon ya koma horo da tawagar, sai aka umarce shi ya ci gaba da yin horo shi kaɗai.
Daraktan wasanni na Atalanta, Tony D’Amico, ya tabbatar da matsalar kafin wasan Lahadi. A cewarsa: “Lookman ba ya yin horo tare da tawaga, kuma muna kara shiga cikin irin wannan yanayi. Abin takaici ne ga kowa, amma haka al’amura suke a yanzu. Za mu duba batun nan bayan kammala kasuwar canja sheƙa.”
Yayin da aka bar Lookman a gefe, sababbin ‘yan wasan da kulob ɗin ta sayo – Nikola Krstovic, Kamaldeen Sulemana, da matashin Honest Ahanor mai shekara 17 – duk sun samu shiga cikin tawaga, alamar cewa Atalanta ta fara shirya sabon tsarin hari ba tare da shi ba.
Duk da wannan rikici, Lookman shi ne ɗan wasan gaba mafi tasiri a Atalanta. Tun zuwansa, ya zura ƙwallaye 52 cikin wasanni 118. Kakarsa ta baya ta fi fice lokacin da ya ci hat trick a wasan karshe na Europa League, abin da ya sa ya samu tarihi a kulob ɗin kuma ya lashe African Ballon d’Or 2024.
Sai dai rabuwar ta kara tsananta, har ma Lookman ya goge dukkan hotunansa da Atalanta daga shafin Instagram ɗinsa – wani mataki da ke nuna tsanani a rikicin.
Lookman yana da kwantiragi har zuwa Yuni 2027, don haka Atalanta na da cikakken iko kan makomarsa. Rashinsa a jerin ‘yan wasan da suka buga wasannin farko biyu na Serie A ya nuna cewa, ko da bai sayu ba, dawowarsa cikin tawaga ba za ta kasance da wuri ba.



