Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana sabon tsari na haɗa matasa cikin ayyukanta ta hanyar amfani da kafafen dijital da masu tasiri a kafafen sada zumunta domin sake fasalta labarin Arewacin Najeriya.
An sanar da wannan sabon salo ne a yayin tattaunawa da aka gudanar a hedikwatar kungiyar da ke Kaduna a ranar Juma’a, a wani ɓangare na shagulgulan cika shekaru 25 da kafa ACF.
Taron, wanda kwamitin ƙara hulɗa da kafafen sada zumunta na kungiyar ya shirya, ya nufi ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ACF da matasa a duniyar dijital.
Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya jagoranci tattaunawar, ya jaddada muhimmancin haɗa matasa wajen ba da labari musamman a wannan zamani da kafafen dijital ke tasiri wajen gina ra’ayi da ɗabi’u.
“Mun gane irin tasirin da matasa ke da shi wajen tsara labari, saboda haka muna buƙatar haɗa su da tafiyar kungiyar domin ci gaba da kare muradun siyasa, tattalin arziki, al’adu da zamantakewar Arewacin Najeriya,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kungiyar na neman haɗin gwiwa da masu tasiri a kafafen sada zumunta domin yaɗa gadon zaman lafiya da tattaunawa, tare da tabbatar da cewa ACF na ci gaba da zama ƙungiya mai hangen nesa.
Ya ce, tunda kashi 70 cikin 100 na matasan Najeriya suna samun bayanai ta yanar gizo, masu tasiri za su iya tallata cikar ACF shekaru 25, nuna ayyukan al’umma, da kuma yada saƙonnin haɗin kai, haɗa matasa da ci gaba.
Shugaban ACF, Mamman Mike Osuman (SAN), ya bayyana wannan sabon salo na dijital a matsayin mai dacewa da zamani, inda ya ce matasa ne suka fi dacewa da wannan sabon aiki.
“Lokaci ya yi da za a mayar da ACF zuwa kafafen dijital musamman na sada zumunta, kuma babu wanda ya fi dacewa da wannan aiki face matasa,” in ji shi.
Sakataren Janar na kungiyar, Murtala Aliyu, ya nuna damuwarsa kan yadda ake yawan nuna Arewa a cikin mummunan haske na talauci da jahilci.
Ya jaddada cewa shiga matasan masu ƙirƙirar abun ciki a kafafen sada zumunta muhimmin mataki ne wajen sauya wannan labari.
Kungiyar ACF ta tabbatar wa masu tasiri cewa ba kawai za su kasance masu yada labarai ba ne, sai dai za a ɗauke su a matsayin abokan hulɗa masu ƙirƙira, inda ra’ayoyinsu za su zama ginshiƙi wajen gina sabuwar siffar Arewa mai kyau da haɗin kai.



