Wike Ya Mallaka wa APC Tsohon Filin Wasa na Area 10 Dake Abuja

Nyesom Wike Minista Birnin Tarayya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bai wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wani muhimmin ɓangare na tsohon Parade Ground da ke Abuja, inda ya mika wa jam’iyyar mallakar fili na dindindin ba tare da biyan kuɗaɗen biliyoyi da dokoki suka tanada ba.

An tsara filin ne tun farko a matsayin wurin gudanar da bukukuwan ranar ’yancin kai, al’adu, wasanni da kuma manyan tarukan siyasa, amma yanzu wani ɓangaren filin ya koma sabuwar hedikwatar APC ta ƙasa.

Takardun hukuma sun nuna cewa a ranar 8 ga watan Agusta, 2025, Hukumar FCT ta ware wani fili mai girman hekita biyu (Plot 4742, Cadastral Zone A01, Garki District), tare da bayar da Right of Occupancy da Certificate of Occupancy cikin rana guda – tsarin da yawanci yakan ɗauki shekaru kafin a kammala shi.

Filin, wanda ya kai murabba’in mita 20,100, an kiyasta kuɗin sa a kimanin Naira miliyan 120.6, tare da ƙarin kuɗaɗen doka da yawanci yakan kai daruruwan biliyoyi. Amma rahotanni sun nuna cewa duk waɗannan kuɗaɗen an yi watsi da su, inda APC ta samu kwangilar haya na shekaru 99 kyauta, ba tare da wani kuɗi ya shiga baitul-malin ƙasa ba.

Wannan na zuwa ne bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar a taron NEC na jam’iyyar a watan Yuli, inda ya bukaci a gina wa jam’iyyar sabuwar hedikwata mai daraja a Abuja.

A halin yanzu, APC na gudanar da ayyukanta daga Muhammadu Buhari House da ke Wuse II, wanda aka saya a 2021 da Naira biliyan 2.5.

Hanzarin da aka yi wajen kammala wannan tsari cikin rana guda ya bambanta ƙwarai da jinkirin da ’yan ƙasa da kungiyoyi ke fuskanta wajen neman filaye a babban birnin ƙasar.

Tun bayan hawansa mulki a 2023, Wike ya mai da manufofin filaye ginshiƙin aikinsa, inda ya dinga kwace filaye da kuma rushe gine-gine bisa hujjar dawo da tsarin babban birnin.

Sai dai masu suka suna zargin cewa yana amfani da wannan dama ne don raba manyan filaye ga abokan siyasa da na kusa da shi a kan sharudda masu sauƙi.