NCAA ta Haramta Amfani da “airplane mode”, ta Umarci Fasinjoji su Kashe Waya

Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayyana cewa dukkan wayoyin hannu dole ne a kashe gaba ɗaya yayin tashin jirgi da kuma lokacin sauka.

Daraktan Hukumar, Kyaftin Chris Najomo, ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki na “National Civil Aviation Security Committee Meeting” da aka gudanar a Abuja a ranar Talata.

Najomo ya ce daga yanzu dukkan fasinjoji wajibi ne su kashe dukkan na’urorin lantarki yayin jirgin yana cikin muhimman matakai na tashi ko sauka, inda hakan ya kawo ƙarshen tsarin amfani da “flight mode” da aka saba amfani da shi tsawon lokaci.

Ya bayyana cewa: “Dukkan wayoyin hannu, na sake maimaitawa, dukkan wayoyin hannu da sauran na’urorin lantarki masu ɗaukar wuta dole ne a kashe su a kalla yayin muhimman lokutan tashi da saukar jirgi. A kashe gaba ɗaya.”

Ya ƙara da cewa babu wani abu da ake kira flight mode a Najeriya daga yanzu, sannan ya umarci kamfanonin jiragen sama su gyara littafin gudanarwar su domin ya nuna wannan sabon doka tare da mika shi ga NCAA don amincewa.

A yayin taron, Najomo ya kuma sanar da jerin matakai masu tsauri da za a ɗauka don dakile yawaitar rashin ladabi da tashin hankali daga fasinjoji a filayen jiragen sama, yana mai gargadin cewa “zamanin yin yadda ake so ya ƙare.”

Ya jaddada cewa NCAA za ta tilasta bin ƙa’idoji sosai daga kamfanonin jiragen sama da fasinjoji, tare da ƙaddamar da wayar da kan jama’a ta hanyar shirye-shiryen rediyo da talabijin.

Najomo ya ce: “Sabuwar hanya za ta fara daga yanzu. Ba za mu ci gaba da yin abin da aka saba ba. Kuma na umarci kamfanonin jiragen sama da su fara horar da ma’aikatansu yadda za su magance rikici da ladabi.”

Ya kuma yi nuni da barazanar tsaro da ake fuskanta a fannin jiragen sama, yana mai cewa rashin bin ƙa’ida daga jama’a, kin aiwatar da tsare-tsaren aiki daga masu hidima, da rashin haɗin kai tsakanin hukumomi na daga cikin manyan matsalolin da ake buƙatar magancewa.

Najomo ya kuma bayyana cewa NCAA za ta gudanar da gwajin gaggawa (mock response exercise) a Legas da Abuja mako mai zuwa don duba shirye-shiryen hukumomi wajen tunkarar matsaloli.

Ya gargadi fasinjoji masu tayar da hankali da cewa za a ɗauki matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da irin wannan hali.

Haka kuma, Daraktan Kariyar Mabukata da Harkokin Jama’a na NCAA, Michael Achimugu, ya ce hukumar za ta ci gaba da aiwatar da doka, inda jami’an tsaro za su tantance yadda za a shawo kan kowace matsala da ta taso.

Ya yi kira ga fasinjoji da su riƙa kai ƙorafe-ƙorafe kai tsaye ga NCAA, yana mai cewa: “Dalilin da hukumar take nan shi ne kare haƙƙin fasinjoji.”

Dangane da wasu matsalolin da suka faru a baya da suka shafi fitattun mutane, Achimugu ya ce hukumar ta magance su cikin tsari, kuma hakan ya zama darasi ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa akwai gibin da ya kamata a cike cikin gaggawa domin tabbatar da tsaron jiragen sama a Najeriya.