Hon. Ali Isa JC Ya Raba Takin Noma Ga Hakiman Yanki Waja

Hon. Ali Isa JC, Makaman Cham

Daga Hassan Muhammad Manga

Hon. Ali Jc PhD da yake wakiltan mazaban Billiri/ Galanga yayi rabon takin zamani a ƙarƙashin jagorancin Hon. Yusuf Manu (Wamban Waja) domin raba takin noma ga hakiman yankin Waja. Wannan karamci ya samo asali ne daga jajircewa da tausayinsa ga al’ummar da yake wakilta.

A jawabinsa, a madadin hakiman yankin, Hakimin Dong, Alhaji Ibrahim Bello, ya gode wa Hon. Ali Isa JC PhD bisa tunawa da su a lokacin jagorancinsa.

Haka zalika, Jama’atu Nasril Islam (JNI) da Kwamitin Da’awar Matasa Musulmi suma sun samu takin noma domin samun sauƙin aikin noma na daminar shekarar 2025.

Bayan rabon kayan, kwamitin ya zarce zuwa garin Dong domin yin jaje ga iyalan tsohon shugaban CAN na Balanga LGA, Reverend Gomna, bisa rasuwar mahaifinsa.

Reverend ɗin a cikin jawabinsa ya gode wa Hon. Ali Isa JC saboda tunawa da iyalinsa a lokacin jimami tare da yi masa addu’ar lafiya da ƙoshin lafiya.