Trends

“Lafiyata kalau,” Akpabio ya karyata jita-jitar rashin lafiya

Godswill Akpabio Yayin dawowa daga kasar waje

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya musanta jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana fama da rashin lafiya mai tsanani.

Akpabio ya iso filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin ƙarfe 4 na safe a ranar Litinin daga London, inda aka tarbe shi a sashen shugabanni na filin jirgin sama tare da wasu sanatoci, hadimai da magoya bayansa.

Isowarsa ya zo ne bayan yaɗuwar rahotannin cewa yana kwance a asibiti a London sakamakon rashin lafiya.

Da yake zantawa da manema labarai a filin jirgin sama, Akpabio ya ce rahotannin ba su da tushe balle ƙaƙa: “Babu wani abu makamancin haka. Lafiyata kalau, na tafi London ne kawai domin ɗan hutun gajere,” in ji shi.

Kafin ɗan hutun da ya yi a Birtaniya, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisun dokoki na duniya karo na shida da aka gudanar a Geneva, Switzerland, daga ranar 29 zuwa 31 ga watan Yuli.

Ya bayyana cewa tawagar Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen yin kira da a ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta haɗin kai tsakanin bangarorin gwamnati.

Shugaban majalisar dattawan ya yi alkawari cewa majalisar za ta gudanar da “aikace-aikacen dokoki masu ƙarfi da inganci” bayan dawowar majalisar daga hutun bazara.