Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kaduna ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agusta a mazaɓun Basawa, Zaria Kewaye da Chikun/Kajuru, inda ta zargi cewa an yi zaɓen cikin tsoro, sayen ƙuri’u da kuma tursasawa da gwamnati ta shirya.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, wacce shugaban jam’iyyar na jiha, Sir Edward Percy Masha ya sanya wa hannu, PDP ta bayyana sakamakon zaɓen da cewa “ba komai ba ne illa kwaikwayo,” tare da sha alwashin daukar matakin shari’a bayan tattaunawa da ‘yan takara, shugabanni da kuma lauyoyinta.
Masha ya bayyana cewa: “Sace ɗan takarar mu da mambobin kwamitin kamfen ɗin Chikun/Kajuru, tare da kwace kuɗaɗen da aka ware domin harkokin sufuri da alawus na wakilai, da kuma sayen ƙuri’u a bainar jama’a, duk suna nuna yadda gwamnatin Uba Sani ta nuna tsananin tsoro da rashin imani.”
PDP ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da dabarun “ƙungiya ta leƙen asiri da salon sojoji” domin murƙushe muradun jama’a, tana mai cewa hakan ya nuna tsoron APC ga karuwar tasirin jam’iyyar adawa a Jihar Kaduna.
Bayan ƙin amincewa da sakamakon, PDP ta nuna damuwa kan ƙarancin fitowar jama’a wajen kada ƙuri’a, tana mai cewa hakan alama ce ta rashin amincewa da tsarin zaɓe.
“Idan wannan mummunan salon siyasa ya ci gaba, matsalar ƙin fitowar jama’a wajen zaɓe za ta ƙara ta’azzara kuma ta kai matsayi mai haɗari kafin shekarar 2027,” in ji sanarwar.
PDP ta kuma yaba wa magoya bayanta bisa juriya da biyayya, tare da yin alkawarin ci gaba da gyara tsarin cikin gida domin ƙarfafa jam’iyyar da samar da nagartaccen wakilci.
“Muna roƙon mutanen Jihar Kaduna da su ci gaba da yarda da kuma goyon bayan PDP. Tare, za mu dawo da mutunci, adalci da sahihin dimokuraɗiyya a jihar mu,” in ji Masha.
Sai dai jim kaɗan bayan sanar da sakamakon zaɓen, sabon kwamishinan yaɗa labarai na jiha, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana nasarar da APC ta samu a matsayin “shaida ta shugabancin dimokuraɗiyya na Gwamna Uba Sani da manufofinsa na kula da jama’a.”
Ya ƙara da cewa da wannan nasara, jam’iyyar APC ta ƙarfafa tasirinta a Kaduna, har ta shiga yankunan da a baya ake ganin cibiya ce ta jam’iyyar adawa.
