Sarkin Zuru a Jihar Kebbi, Manjo Janar mai ritaya Muhammadu Sani Sami, ya rasu a daren Asabar.
Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu na jihar Kebbi, Alhaji Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Bisa ga sanarwar, Sarkin ya rasu yana da shekara 81 a wani asibiti da ke birnin London bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Allah Ya jikansa. Ya bar mata huɗu da ’ya’ya bakwai.



