Ministan Ayyuka na Tarayya, Sanata Dave Umahi, ya bayyana cewa duk da cewa yankin Kudu maso Gabas zai samu damar fitar da shugaban kasa a nan gaba, wannan dama ba za ta zo ba a zaben shekarar 2027.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Umahi ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas da su hada kai wajen mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin samun wa’adin mulki na biyu, yana mai jaddada cewa shugaban kasar yana nuna adalci da kulawa ga yankin ta fuskar ayyukan raya kasa.
Umahi ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rahoto da aka wallafa a kafar yanar gizo (ba daga Daily Trust ba), wanda ya ce ana kokarin bata sunan gwamnatin Tinubu da zargin watsi da yankin.
“Ina fahimtar cewa lokacin siyasa ya matso, kuma wasu mutane sun dauki hanyar yaudarar jama’a marasa masaniya,” in ji Umahi. “Suna son su nuna kamar su ne jarumai, amma suna kau da kai daga manyan ayyukan ci gaba da shugaban kasa ke aiwatarwa a fadin kasar nan.”
Ya ce ya riga ya umurci dukkan daraktocin yankuna a Ma’aikatar Ayyuka da su koma wuraren ayyukan da ke gudana domin tattara bayanai kan sabbin ayyuka da wadanda aka gada, don nuna irin aikin da ake gudanarwa a karkashin mulkin Tinubu, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko yadda aka kada kuri’a ba.
Umahi ya bayyana cewa shugaba Tinubu na amfani da tsarin rarraba ayyuka cikin adalci don sake gina hadin kan kasa da dawo da amincewar jama’a ga gwamnati. “Sai wanda ya bude ido ne zai gane hasken sauyin da ke faruwa a Najeriya,” in ji shi.
Kan batun shugaban kasa daga Kudu maso Gabas, Umahi ya shawarci ‘yan Igbo da su maida hankali wajen gina kawancen siyasa da sauran yankuna maimakon dagewa kan samun mulki a 2027.
“Dole ne mu guji sake shan kaye ta hanyar ruɗu,” in ji Umahi. “Shugaban kasa na bukatar samun goyon bayan kashi 90% daga Kudu maso Gabas domin karfafa dangantakarmu da shi.”
Ya gargadi al’ummar yankin da su guji siyasar gaba, yada jita-jita da kalaman rarrabuwar kawuna. “Idan muna fatan samun shugaban kasa daga yankinmu, dole ne mu guji siyasar kiyayya da son zuciya,” Umahi ya kara da cewa. “Mu tallafa wa sauran yankuna, kuma da ikon Allah, wata rana su ma za su tallafa mana.”
Ya jaddada cewa dole ne a ba Shugaba Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas, yana mai cewa: “Wata rana za mu zama na daya — amma ba a shekarar 2027 ba.”
Umahi ya yaba da kokarin gwamnonin Kudu maso Gabas wajen ci gaban yankunansu, tare da bukatar ci gaba da hadin gwiwa da gwamnatin tarayya.
Jawabinsa na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake kara samun kiran da ke bukatar Kudu maso Gabas ta fitar da shugaban kasa a 2027, musamman bayan dan takarar jam’iyyar Labour Party a 2023 kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takara.
