Sakamakon Jarrabawar WASSCE: Kashi 38.32% Kacal Suka Yi Nasara

Hukumar shirya jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) na shekarar 2025 ga daliban makarantu, inda aka samu gagarumar faduwa idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Daga cikin dalibai 1,969,313 da suka zauna jarrabawar, 754,545 kacal ne – wanda ke wakiltar kashi 38.32% – suka samu akalla darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi. Wannan na nuni da raguwar nasara idan aka kwatanta da kashi 72.12% da aka samu a 2024.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Legas, Shugaban Ofishin WAEC na kasa, Dr. Amos Dangut, ya bayyana cewa wannan raguwar ba ta rasa nasaba da sabon tsarin da hukumar ta kirkiro wajen canza yadda ake bayar da tambayoyin “objective” a muhimman darussa.

“A wannan shekarar, mun dauki matakin yin tambayoyin da ke da lamba-lamba daban-daban ga dalibai, wanda hakan ya rage yawan yin hadin gwiwar karya (collusion) a jarrabawa,” in ji Dangut. Ya kara da cewa “duk da cewa akwai raguwar maki a bangaren tambayoyin objective, bangaren rubutu (essay) ya kasance daidai da shekarun da suka gabata.”

Jarrabawar ta gudana daga 24 ga Afrilu zuwa 20 ga Yuni, 2025. WAEC ta kuma gabatar da sabon tsarin tantance sakamako na zamani da ke faruwa a lokaci guda (real-time digital scoring system) tare da ba wa dalibai zabin amfani da takarda da fensir ko kuma jarrabawar kwamfuta (CBT), a wani mataki na cimma burin dijital gaba daya kafin 2026.

Dangut ya bayyana cewa, “Wannan jarrabawa ta sanya mu cikin sahun gaba na hukumomin jarrabawa da suka gudanar da gwajin cancanta ta hanyar kwamfuta.”

Daga cikin yawan daliban da suka zauna jarrabawar, kashi 77.06% ne aka tantance nasu gaba daya kuma aka fitar, yayin da sauran kashi 22.94% ke cikin tsarin tantancewa saboda matsalolin fasaha.

A wani yunkuri na yaki da magudin jarrabawa, WAEC na rike sakamakon dalibai 192,089 – wanda ke wakiltar kashi 9.75% – saboda laifukan da suka shafi cin hanci da magudi, adadi wanda ya ragu daga kashi 11.92% a 2024.

“Wadannan masu laifi sun zama tamkar tarkon WAEC. Wasu ma suna amfani da sunanmu wajen yada sakonni karya. Mun kama wasu daga cikinsu kuma za a hukunta su bisa ka’ida,” in ji Dangut.

Ya kuma gargadi jihohin da har yanzu ke bin WAEC bashi cewa ba za su iya duba sakamakon daliban da suka dauki nauyi ba har sai sun biya dukkan kudaden da ake binsu.

A cikin wadanda suka samu nasara da darussa biyar da suka hada da Turanci da Lissafi, mata sun fi maza da kashi 53.99% na yawan wadanda suka ci gaba, yayin da maza suka samu kashi 46.01%.

Jarrabawar ta kuma karbi dalibai masu bukatu na musamman guda 12,178.

Sakamakon ya fito ne a hukumance a ranar Litinin, 4 ga Agusta, 2025, kuma dalibai na iya dubawa ta shafin WAEC: http://waecdirect.org.