Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba wa dukkan ’yan wasan ƙungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, lambar girmamawa ta ƙasa saboda nasarar da suka samu a gasar 2025 Women’s Afrobasket da aka gudanar a Côte d’Ivoire.
Shugaban ƙasar ya kuma ba kowace ’yar wasa kyautar dala $100,000, yayin da mambobin kwamitin fasaha (technical crew) suka samu ƙarin dala $50,000 kowannensu.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu a wajen bikin tarbar ƙungiyar a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin, ne ya bayyana wannan yabo da kyauta.
Baya ga kuɗin da za a ba su, kowanne daga cikin ’yan wasa da jami’an ƙungiyar za su samu gida a babban birnin tarayya (FCT).
A ranar Lahadi, Najeriya ta doke Mali da ci 78-64 a wasan ƙarshe da aka gudanar a Palais des Sports de Treichville da ke Abidjan.
Wannan nasara ta sanya Najeriya ta zama ƙasa ta farko da ta lashe kofin Afrobasket na mata sau biyar a jere.
Ƙungiyar D’Tigress ta samu tikitin kai tsaye zuwa gasar FIBA Women’s World Cup ta 2026 da za a yi a birnin Berlin, ƙasar Jamus.
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya karrama kowacce ’yar wasa a cikin tawagar da ta lashe gasar da lambar Officer of the Order of the Niger (OON).
Cikin manyan baki da suka halarci taron har da Uwargidar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu; Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa; Sanata Garba Maidoki, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Matasa da Ci gaban Wasanni; da Kabiru Amadou, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Wasanni.





