Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai cewa wannan labari karya ne kuma ba shi da tushe.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Sanata Yar’Adua ya sake jaddada cikakken biyayyarsa ga jam’iyyar APC tare da bukatar al’umma da kafafen yada labarai su yi watsi da abin da ya kira “kanun labaran kirkir-kirkir” da ke nufin yaudarar ’yan Najeriya.
“Ina so in bayyana a fili cewa har yanzu ina da cikakken goyon baya da biyayya ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ina rokon kafafen yada labarai da su yi watsi da duk wani labari da ke nuna cewa na sauya sheka daga jam’iyyar,” in ji shi.
Sanatan dan asalin jihar Katsina, wanda ke shugabantar Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Sojoji da kuma Kungiyar Sanatocin Arewa, ya bayyana cewa ba kowane dan gidan Yar’Adua ba ne ke da nasaba da siyasar sa.
“Ya kamata a fahimta cewa ba kowanne mutum da ke dauke da sunan Yar’Adua ke da alaka da ni a fagen siyasa ba,” in ji shi, yana zargin wasu kafafen yada labarai da kokarin tayar da hankali ta hanyar yada labaran karya.
Sanata Yar’Adua ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana goyon bayansa ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana yabawa kokarinsa wajen kara kason kudade ga jihohi da kananan hukumomi, inganta ababen more rayuwa da kuma karfafa tsaron kasa ta hanyar daukar sabbin ma’aikata.
“A matsayina na jagoran siyasa, ina ganin wajibi ne mu hada kai da Shugaban Kasa domin ganin wannan gwamnati ta yi nasara kuma talaka ya ji dadin sauye-sauyen da gwamnatin APC ke aiwatarwa,” ya kara da cewa.
Ya kammala da jaddada aniyarsa ta ci gaba da aiki da dukkan shugabanni domin tabbatar da dunkulewar kasa da ci gaba karkashin jagorancin APC.
“Har yanzu ina da cikakken biyayya ga jam’iyyar APC, kuma zan ci gaba da aiki da shugabanni domin hadin kan kasa, cigaba da walwalar dukkan ’yan Najeriya.”
