Trends

LG Polls: Rudani Yayin da Mambobin PDP Suke Fitowa a Matsayin ‘Yan Takarar APC a Rivers

Ana cikin wani hali na rudani a Jihar Rivers gabanin zaben kananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Agusta, 2025, bayan da aka gano cewa wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun bayyana a matsayin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi na All Progressives Congress (APC) a yawancin kananan hukumomin jihar.

Bincike ya nuna cewa daga cikin kananan hukumomi 23 da ke jihar, mambobin PDP ne suka bayyana a matsayin ‘yan takarar APC a kananan hukumomi 12 bayan kammala zabukan fidda gwani da aka gudanar a ranar Asabar.

Kananan hukumomin da wannan al’amari ya shafa sun hada da: Asari Toru, Ikwerre, Khana, Tai, Degema, Bonny, Oyigbo, Omuma, Ogu/Bolo, Gokana da Etche.

Wakilinmu ya lura cewa wasu daga cikin wadanda aka bayyana a matsayin ‘yan PDP kuma suka ci zabe a jam’iyyar su sun fito ne daga Emohua, Birnin Port Harcourt da Obio/Akpor.

A halin yanzu kuwa, akwai rahotanni da ke nuna cewa manyan jam’iyyun siyasa a Jihar Rivers, da suka hada da African Democratic Congress (ADC), Action Peoples Party (APP) da kuma wani bangare na APC, na iya kauracewa wannan zaben na kananan hukumomi.

A tuna cewa a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024, jam’iyyar APP wacce ke samun goyon bayan gwamna mai murabus Siminalayi Fubara, ta lashe kananan hukumomi 22 daga cikin 23 a fadin jihar.

Sai dai a hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar 25 ga Fabrairu, 2025, an soke nasarar zabukan, inda kotun ta bayyana cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Rivers (RSIEC) ba ta bi dokar bayar da sanarwar kwanaki 90 kafin zabe kamar yadda Dokar Zabe ta tanada ba.

Da yake magana da manema labarai a Port Harcourt, kakakin jam’iyyar ADC a jihar, Chief Luckyman Egila, ya ce har yanzu jam’iyyar ba ta yanke shawara kan ko za ta shiga zaben ba, yana mai cewa za a yi taron masu ruwa da tsaki kafin a dauki matsaya.

“A cikin kwanaki masu zuwa, shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC za su gana don tantance matsayin jam’iyya kan ko za mu shiga zaben ko a’a. Bayan wannan taro ne za mu sanar da matsayarmu,” in ji Egila.

Haka zalika, kakakin bangaren Chief Emeka Beke na jam’iyyar APC a jihar, Hon. Darlington Nwauju, ya bayyana cewa shigar jam’iyyar APC cikin zaben na dogara ne da warware rikicin cikin gida da kuma samun cikakken sahalewar RSIEC.

“Mun dauki matsaya ne bisa la’akari da wasu kura-kurai da RSIEC ta tafka dangane da rashin amincewa da shugabannin jam’iyyar da aka tabbatar da sahihancinsu,” in ji Nwauju.

Ya ci gaba da cewa, “Amma bayan ganawar da muka yi da shugabannin jam’iyyar na kasa, ina ganin za mu samu daidaito domin kada a jefa makomar jam’iyya cikin hatsari saboda wasu mutane da ke da son kai da bukatun kansu na siyasa.”

Halin da ake ciki na kara dagula yanayin siyasa a Jihar Rivers gabanin zaben kananan hukumomi, inda jam’iyyun ke kokawa da rikice-rikice na cikin gida da kuma zargin mummunan tsari daga hukumar zabe ta jihar.