Trends

Hadin Kai Yan Nigeriya: El-Rufai Ya Gargadi Yan Nigeriya Da Kada Su Zabi Tinubu a Zaben 2027

Nasir El-Rufai Tsohon Gwamnan Kaduna

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi gargadin cewa sake bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) dama a 2027 zai iya lalata ginin hadin kan al’umma da kwanciyar hankali a Najeriya.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani taron wayar da kan al’umma da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta shirya a jihar Sokoto, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga wannan gagarumin motsi na adawa.

Ya ce zai hada kai da sauran ‘yan Najeriya domin ganin an kawar da APC daga mulki a zabe mai zuwa.

“Ina ganin idan muka bar wannan jam’iyya da gwamnati ta ci gaba da mulki a karo na biyu, ragowar hadin kan al’umma da muke da shi a Najeriya zai rushe gaba daya – kuma hakan na iya jefa kasar cikin wani hali. Wannan gwagwarmaya ce don ceton rayukanmu da makomar kasar nan,” in ji El-Rufai.

Ya ce dawowarsa siyasa ba don wata muradin kansa ba ce, sai domin ceto kasar daga abin da ya kira gazawar gwamnatin yanzu.

“Ina siyasa ba don na samu wani abu ba. Ina siyasa ne domin hidimtawa al’umma. Idan gwamnati ba ta yi wa jama’a aiki ba, to, hakki ne na a matsayina na dattijo in fito in soki, in kuma dauki matakin da zai daidaita lamura,” El-Rufai ya bayyana.

El-Rufai ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ADC ta hada gwiwa da wasu manyan ‘yan siyasa da ke adawa da manufofin APC, yana mai cewa taron Sokoto na daya daga cikin matakan kaddamar da yunkurin kasa baki daya na wayar da kai da tunkarar gwamnati mai ci.

“Muna nan a Sokoto domin fara hadin gwiwar tunkarar APC a kowanne mataki – daga matakin jihohi har zuwa gwamnatin tarayya a Abuja,” in ji shi.

Tsohon gwamnan, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar a watan Maris 2025, inda ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), yana mai bayyana rashin jin dadinsa da