A fafatawar karshe mai cike da gasa, Skyline Football Club ta yi nasara akan Unique Football Academy da ci 3-0 a wasan karshe na gasa da aka dade ana jira.
An buga wasan a filin kwallon kafa na Dawaki Football Stadium dake Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda Skyline FC ta nuna kwarewa da dabaru masu kayatarwa har ta dauki kambun zakarun gasar.
Kodayake Unique FA ta yi kokari wajen neman daidaita sakamakon, tsaron Skyline ya tsaya daram, suka ci gaba da matsa musu har zuwa karshen wasa.
Kocinsu, Chile Innocent, ya yabawa ’yan wasansa bisa jajircewa da hadin kai, tare da nuna godiya ga masu shirya gasar da kuma abokan karawa.
Ya ce:
First TV ta ruwaito cewa babban jami’in gudanarwa na 043 Football Club, Nwovu Friday Simon Gabby, shi ne ya shirya gasar domin gano sabbin hazikan ’yan wasa da kuma shirya su don manyan damammaki a nan gaba.

An fara gasar ne a ranar 10 ga Agusta, 2025, inda kungiyoyi 13 daga fadin Babban Birnin Tarayya suka shiga fafatawa.
Bayan samun nasara, Skyline FC ta karbi kofin gasar tare da kyautar kudi Naira 500,000, yayin da Unique FA da ta tashi a matsayi na biyu ta samu Naira 300,000 a matsayin lada.
“Wannan nasara shaida ce ta kokari da jajircewar ’yan wasanmu. Muna alfahari da abin da muka cimma, kuma muna sa ran murnar tare da magoya bayanmu. Mun shigo da niyyar nasara, muka samu. Muna godiya ga 043 Football Club da suka shirya wannan gasa, wacce ta ba mu dama mu nuna kwarewarmu. Kuma dole mu yaba wa abokan karawa Unique FA saboda su ma kungiya ce mai karfi da ta sanya wasan ya kasance mai matukar zafi. Ga magoya baya da masu kallo, muna cewa nagode kwarai.”







