Trends

Masana Sufurin Jirage Sun Yi Watsi da Tallafin Naira Biliyan 60

NCAA NCAA

Masana harkokin sufurin jiragen sama da ke ƙarƙashin ƙungiyar Aviation Safety Round Table Initiative (ASRTI) sun soki rahotannin da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta rage wa kamfanonin jiragen sama wasu kuɗaɗen bashi da suka kai Naira biliyan 60, suna mai cewa matakin bai magance matsalolin da ke addabar fannin sufurin jiragen sama a Najeriya ba.

Shugaban ASRTI, Ademola Onitiju, ya ce rangwamen bai rage farashin man jirgin sama na Jet A1 ba, bai kuma rage basussukan kamfanonin jiragen sama ko farashin tikitin tafiya ba, lamarin da ya ci gaba da ɗora wa kamfanoni da fasinjoji nauyin tsadar rayuwa.

Ya bayyana cewa fannin sufurin jiragen sama na cikin gida a Najeriya na fuskantar babbar matsala sakamakon tashin gwauron zabi da farashin man Jet A1 ke yi.

A cewarsa, wannan ne ya sa kuɗin man fetur ya kai kusan rabin dukkan kuɗaɗen gudanar da ayyukan kamfanonin jiragen sama, tare da tilasta musu ƙara farashin tikiti zuwa matakin da yawancin ‘yan Najeriya ba za su iya ɗauka ba.

Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu ana sayar da litar man Jet A1 tsakanin Naira 1,650 zuwa Naira 2,037, wanda ke cin kusan rabin kuɗaɗen gudanar da ayyukan kamfanonin jiragen sama.

Duk da rage basussukan da gwamnati ta yi, farashin tikitin jiragen sama bai sauka ba, yayin da sauran ɓangarorin da ke da alaƙa da harkar sufurin jiragen sama kamar jigilar kaya, yawon buɗe ido da otal-otal ba su samu wata fa’ida mai ma’ana ba.

Onitiju ya bayyana tallafin Naira biliyan 60 a matsayin wani mataki marar tasiri, yana mai ba da shawarar ƙaddamar da wani shiri mai suna Fuel-for-Stability Programme, wanda zai bai wa matatun mai na cikin gida ɗanyen mai kai tsaye domin tabbatar da wadataccen man jiragen sama da rage tsadarsa ga kamfanonin jiragen sama na cikin gida.

Ya ce manufar ba wai kawai rage farashin mai zuwa Naira 300 ko ɗan fiye da haka ba ce, illa dai samar da tsayayyen tsarin samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida domin rage kuɗaɗen aiki, rage farashin tikiti, ƙara yawan fasinjoji, inganta ribar kamfanonin jiragen sama da kuma ƙarfafa hukumomin kula da harkokin sufurin jiragen sama.

Ƙungiyar ASRTI ta jaddada cewa samar da sauƙin sufuri ta jirgin sama zai buɗe ƙarin damammakin tattalin arziki, ya faɗaɗa damar samun ayyukan jiragen sama ga jama’a, tare da mayar da zirga-zirgar jiragen sama abin da talakawa za su iya amfani da shi.

Onitiju ya ambaci ƙasashe irin su India, Turkey, Indonesia da Brazil a matsayin misalan ƙasashen da suka inganta harkokin sufurin jiragen samansu ta hanyar mayar da hankali kan sauƙaƙe farashi da aiwatar da gyare-gyare masu ɗorewa.

Duk da yabawa ƙoƙarin gwamnati na dawo da amincewar masu ba da hayar jiragen sama na ƙasashen waje da kuma tallafa wa cibiyoyin gyaran jiragen sama na cikin gida, ASRTI ta ce har yanzu akwai buƙatar aiwatar da tsare-tsare masu ƙarfi da za su sa harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya su zama masu gasa a duniya kuma masu ɗorewa.