Grid ɗin wutar lantarki na ƙasa ya sake rushewa a ranar Laraba, lamarin da ya jefa sassa daban-daban na ƙasar cikin duhu tare da katse wutar lantarki ga miliyoyin gidaje da kasuwanci.
Bincike ya nuna cewa samar da wutar lantarki ya faɗi ƙwarai daga sama da megawatt 4,500 zuwa kusan megawatt 24 da misalin ƙarfe 1:30 na rana.
Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa dukkan kamfanonin samar da wutar lantarki 23 da ke haɗe da grid ɗin sun rasa fitar da wuta yayin faruwar lamarin, wanda ya haifar da rashin rarraba wuta ga dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 na ƙasar.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a bayyana a hukumance musabbabin rushewar grid ɗin ba, inda Kamfanin Watsa Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN) bai fitar da cikakken bayani kan lamarin ba.
Wannan shi ne karo na farko da aka samu rushewar grid a shekarar 2026, kuma ya faru ne makonni kaɗan bayan irin wannan matsala da ta auku a ranar 29 ga Disamba, 2025, wadda ita ma ta haddasa katsewar wuta a faɗin ƙasa.
A ‘yan shekarun nan, an danganta yawan rushewar grid ɗin wutar lantarki da matsalolin fasaha, rashin kyakkyawan kulawa ga kayayyakin watsa wuta, da rashin daidaito a samar da wutar lantarki.
Masu ruwa da tsaki a bangaren wutar lantarki sun dade suna kira ga Gwamnatin Tarayya da masu gudanar da harkokin wutar lantarki da su samar da ƙarin matakan kariya da tsare-tsare domin hana ci gaba da faruwar irin waɗannan matsaloli.
Yayin da jama’a ke jiran bayani a hukumance, wannan sabon rushewa ya sake tayar da damuwa kan raunin tsarin wutar lantarki na Nijeriya da kuma ikon sa na biyan buƙatar ƙasar na samun ingantacciyar wutar lantarki mai ɗorewa.
