Wani ƙarfi daga cikin jam’iyyar APC mai mulki, wanda ya samo asali daga tsohuwar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), ya buƙaci a bar musu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027 tare da tabbatar da cewa za su samu tikitin shugabancin ƙasa na jam’iyyar a 2031.
Ƙungiyar ta bayyana buƙatarta ne a ƙarƙashin sunan Association of Former ANPP Members, inda ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mutunta yarjejeniyar rabon madafun iko da aka cimma lokacin haɗaɗɗiyar jam’iyyar APC a shekarar 2013.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, ƙungiyar ta gargadi jam’iyyar APC cewa ci gaba da wulakanta su na iya sa su sake nazarin matsayin su cikin jam’iyyar.
“Tsoffin ‘yan ANPP sun yi babban sadaukarwa domin nasarar jam’iyyar APC. Adalci ya wajabta a saka mu daidai ta hanyar bai wa kowa hakkin sa,” in ji ƙungiyar.
Da yake gabatar da matsayar ƙungiyar, Shugaban ƙasa na ƙungiyar kuma tsohon Mataimakin Shugaban ANPP (Kudu), Farfesa Vitalis Orikeze Ajumbe, ya buƙaci Shugaba Tinubu da kada ya zabi wani mataimaki daga waje ko wata ɓangare daban da na ANPP a zaɓen 2027.
“Wannan tikitin da kake kai zai ji haushi idan ka zabi wani daga waje a matsayin mataimakin shugaban ƙasa,” in ji Ajumbe.
Ya bayyana cewa wannan buƙata ce da aka cimma ta yarda bayan wani taron shugabannin ƙungiyar da suka duba makomar su cikin APC.
“’Yan sa’o’i da suka gabata, mun kammala taron shugabanni na ƙungiyar tsoffin ‘yan ANPP a cikin APC a madadin miliyoyin mambobinmu a fadin ƙasa, inda muka yi nazari kan matsayarmu a jam’iyyar,” in ji shi.
Ajumbe ya zargi gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da nuna wariya ga ɓangaren ANPP tsawon shekaru takwas da ya yi a mulki, duk da cewa ANPP na daga cikin manyan masu haɗa jam’iyyar APC.
“Buhari bai cika cancanta da kwarewa a siyasa ba kamar Shugaba Bola Tinubu wanda ya taso daga siyasa har ya kai wannan matsayi,” Ajumbe ya bayyana.
“Idan siyasa gaskiya ce da adalci, to dole ne a bai wa ‘yan ANPP manyan mukamai tun daga lokacin gwamnatin Buhari. Amma abin da muka samu kawai shine wulakanci da watsi da mu.”
Ya jaddada cewa ANPP na da fitattun ‘yan siyasa da suka taka rawa a gwamnatin Najeriya, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum; da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni. Haka kuma akwai tsofaffin gwamnoni, sanata da wakilai da dama da suka fito daga ANPP.
Duk da irin wannan cancanta, Ajumbe ya koka da cewa ba a bai wa ɓangaren ANPP wani muhimmin matsayi a gwamnatin Tinubu ba.
“Daga cikin duka nade-naden mukamai da aka yi karkashin Tinubu – tun daga ministoci, shugabannin hukumomi, da daraktoci – ba a bai wa ANPP ko ɗaya daga cikin manyan matsayi ba,” in ji shi.
Ya ƙara jaddada bukatar su ta cewa dole ne kujerar mataimakin shugaban ƙasa ta kasance a hannun ANPP, tare da tabbatar da cewa tikitin shugaban ƙasa na 2031 ma na ANPP ne.
“Kujerar mataimakin shugaban ƙasa dole ta kasance a hannun tsoffin ‘yan ANPP a cikin APC kasancewar su na daga cikin manyan da suka kafa jam’iyyar,” in ji Ajumbe.
“Tunda CPC ta rike mulki na shekaru takwas karkashin marigayi Buhari, yanzu ACN ke da shugabanci. To a bisa adalci da gaskiya, ya kamata shugaban kasa mai ci ya mika mulki ga ANPP a 2031.”
