Trends

Kudin Fansa: ‘Yan Bindiga Sun Yanka Mutane 35 da Suka Sace a Zamfara

Hoton Yan Ta'adda

‘Yan bindiga sun kashe mutane 35 daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su a ƙauyen Banga, da ke ƙaramar hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, bayan iyalansu sun kasa biyan kudin fansa da suka kai naira miliyan 35.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka kashe na daga cikin mutum 53 da aka sace watanni da suka gabata, inda ‘yan bindigar suka nemi naira miliyan ɗaya (₦1m) akan kowanne mutum.

A cewar wani mazaunin ƙauyen Banga, Sani Suleiman, mutum 18 daga cikin waɗanda suka biya kudin fansa an sako su, yayin da saura 35 aka kashe su ta hanyar yanka. Suleiman ya bayyana lamarin da cewa abu ne mai tayar da hankali, yana mai cewa waɗanda suka tsira sun shaida yadda aka kashe sauran da ruwan sanyi.

One thought on “Kudin Fansa: ‘Yan Bindiga Sun Yanka Mutane 35 da Suka Sace a Zamfara

Comments are closed.