Shugaban Kasar Gambiya, Adama Barrow, a ranar Juma’a ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a garinsa na Daura, Jihar Katsina.
Shugaba Barrow, wanda ya isa Katsina don ziyarar ta’aziyyar, ya samu tarba daga Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari, tare da wasu daga cikin ‘yan uwan marigayi Buhari.
Yayin da yake bayyana jimaminsa, Barrow ya bayyana marigayi Buhari a matsayin ginshikin dimokuradiyya da kuma mai jajircewa wajen kare martabar kasar Gambiya.
“Shugaba Buhari ya tsaya tsayin daka tare da mu da al’ummar Gambiya domin tabbatar da cewa an mutunta zabenmu na dimokuradiyya kuma an aiwatar da sakamakonsa gaba daya,” in ji shi.
Shugaban na Gambiya ya kara da cewa Buhari ya fi shugaba a wajensa, yana cewa:
“Kullum da na hadu da Buhari, ina ganin uba, dan uwa, da kuma kawu a gabana.”
Ya yaba da rawar da marigayi Buhari ya taka wajen wanzar da zaman lafiya da dimokuradiyya a nahiyar Yammacin Afrika ta hannun ECOWAS, Tarayyar Afrika (AU), da kuma a matakin duniya baki daya.
“Ina jin wani nauyin godiya bisa abin da Shugaba Buhari ya yi — ba wai ga Gambiya kadai ba, har da ECOWAS, Tarayyar Afrika da kuma martabar Najeriya a idon duniya.
“Ya tsaya tsayin daka wajen kare dimokuradiyya, ‘yanci da adalci,” in ji Barrow.
Shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari da daukacin ‘yan Najeriya, yana mai cewa:
“Muna mika sakon ta’aziyyarmu daga zuciya ga iyalansa da kuma dukan ‘yan Najeriya bisa rasuwar wannan babban mutum — wanda ya taimaka wajen gina mu zuwa ga inda muke yau.”
A nasa bangaren, Alhaji Abdullahi Garba-Faskari ya bayyana ziyarar Barrow a matsayin kyakkyawan misali na zumunci da ‘yan uwa tsakanin kasashen Afrika.
Ya ce gudunmawar Buhari wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya da ma nahiyar Afrika za ta ci gaba da kasancewa tarihi.
Da yake mayar da martani a madadin iyalan, Yusuf Buhari, dan marigayi shugaban kasa, ya nuna godiya matuka bisa ziyarar.
Ya bayyana ziyarar a matsayin alamar zumunci da dangantaka mai karfi tsakanin Najeriya da Gambiya, da kuma gado mai dorewa da marigayi Buhari ya bari a Afrika. (NAN)
