Trends

Sarkin Gusau Ibrahim Bello Ya Rasu

Sarkin Gusau Dr Ibrahim Bello

Mai Martaba Sarkin Gusau, Alhaji Dr. Ibrahim Bello, ya rasu yana da shekaru 71. Ya rasu ne da safiyar ranar Juma’a a birnin Abuja bayan doguwar jinya.

Rasuwar wannan babban basarake ta jefa Masarautar Gusau da daukacin jihar Zamfara cikin jimami da alhini. Daga cikin wadanda suka fara nuna alhini akwai Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, wanda ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi gare shi kai tsaye.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris Bala, ya fitar, Gwamna Lawal ya bayyana marigayin Sarkin Gusau a matsayin shugaba nagari, mai jajircewa da kishin cigaban al’umma.

“Ina matuƙar alhini da karɓar labarin rasuwar mahaifinmu, Mai Martaba Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello,” in ji Gwamna Lawal.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Masarautar Gusau, Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, da kuma dangin marigayin, yana mai cewa rasuwar Sarkin babban gibi ne ba kawai ga jihar ba har ma da kasa baki ɗaya.

“Marigayin Sarkin ya kwashe shekaru goma yana gudanar da mulki tun daga lokacin da ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15 a ranar 16 ga Maris, 2015. Ya shugabanci masarautar da tsantsar sadaukarwa, imani da kyakkyawar niyya wajen tallafa wa jama’arsa,” in ji Gwamnan.

Allah Ya jikan Sarkin da rahama, Ya ba da hakuri ga iyalan da ya bari da daukacin al’ummar Zamfara.