Shugabannin jam’iyyar PDP a Jihar Osun sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Ademola Adeleke tare da amincewa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.
Wannan mataki ya fito ne daga wata sanarwa da aka fitar bayan wani taron manyan shugabannin jam’iyyar PDP da aka gudanar a gidan gwamnati dake Osogbo a ranar Litinin, 21 ga Yuli, 2025.
Taron ya biyo bayan rade-radin da ake yi na yiwuwar sauya sheka da Gwamna Adeleke ke shirin yi zuwa jam’iyyar APC. A cewar sanarwar, an gudanar da shawarwari da dama da suka hada da na sarakunan gargajiya, ma’aikata, ’yan fansho, shugabannin addinai, shugabannin kasuwa, mambobin jam’iyya da sauran jama’ar Jihar Osun.
Sanarwar ta jaddada cewa “duk siyasa na cikin gida ce,” tana mai bayyana bukatar sanya muradun jama’ar Osun da mambobin PDP a gaba wajen yanke hukunci na siyasa.
Cikin sanarwar, an karyata rahotannin da ke cewa Gwamna Adeleke yana shirin ficewa daga PDP zuwa APC, inda aka bayyana hakan a matsayin jita-jita da ba ta fito daga bakin gwamnan ba. Har ila yau, an bayyana cewa martanin da wasu jiga-jigan APC suka mayar ya kasance mai cike da kalaman batanci da cin mutunci a kafafen sada zumunta da gidajen talabijin.
Duk da cewa wasu mambobin PDP sun bayyana shirin bin Adeleke ko’ina bisa biyayya, yawancin mambobin jam’iyyar sun nuna rashin amincewa da barin jam’iyyar zuwa APC.
“PDP a Jihar Osun har yanzu ita ce mafi karbuwa da farin jini a tsakanin jama’a,” in ji sanarwar.
Taron ya yanke wasu muhimman matsaya kamar haka:
Goyon bayan Tinubu a 2027: PDP ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda asalinsa daga Osun ne, a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Adeleke ya sake tsayawa takara a 2026: An amince da Gwamna Adeleke ya sake tsayawa takarar gwamnan Osun a karkashin tutar PDP a zaben 2026.
Tabbatar da Aminci ga PDP: An bukaci dukkan mambobi su zauna a cikin jam’iyyar PDP tare da kin yarda da duk wani yunkurin sauya sheka.
Yaduwar Sanarwa: An umarci shugabannin jam’iyyar su baza wannan sanarwa zuwa matakin ƙananan hukumomi da kananan mazabu na jam’iyyar.
Ci gaba da Ayyuka: An shawarci Gwamna Adeleke da ya ci gaba da aiwatar da shirin ci gaba na maki biyar (Five Point Agenda) ba tare da wata tangarda ba.
Sanarwar ta samu sa hannun Gwamna Adeleke da wasu jiga-jigan PDP guda 27 a jihar, ciki har da tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola, mataimakin gwamna Prince Kola Adewusi, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jiha Adewale Egbedun, da wasu ‘yan majalisar dokoki na jiha da tarayya – na yanzu da na baya.



