Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyu hudu bisa gazawarsu wajen cika sharuddan kundin tsarin mulki da dokokin kasa suka gindaya ga jam’iyyun siyasa.
Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda ya ce jam’iyyun sun kasa samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’un da ake bukata a babban zaben da ya gabata, lamarin da ya saba da tanade-tanaden doka.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun hada da ADC, Accord (A), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Tun da farko, Mai shari’a Lifu ya yi watsi da dukkanin korafe-korafen farko da wadanda ake kara suka gabatar, sannan ya umarci INEC da kada ta bari wadannan jam’iyyu su shiga zabuka masu zuwa, ciki har da babban zaben shekarar 2027, saboda sun kasa kai matsayin da doka ta tanada.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of the National Forum of Former Legislators ce ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026 a gaban kotun kan jam’iyyun guda biyar.
Kungiyar ta hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a cikin karar, yayin da ta sanya INEC a matsayin wanda ake kara na farko.
Masu karar sun yi zargin cewa jam’iyyun sun kasa cika sharuddan kundin tsarin mulki da suka shafi yaduwar tasirin jam’iyya da kuma yadda suka taka rawa a zabuka.
Sun kuma bayyana cewa doka ta tanadi cewa jam’iyyun siyasa su samu akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’u a zabukan da aka kayyade domin ci gaba da kasancewa a matsayin halastattun jam’iyyun siyasa.
Saboda haka, sun roki kotun da ta umarci a soke rajistar jam’iyyun, suna mai cewa babu daya daga cikinsu da ya gabatar da hujjoji masu karfi da za su rusa korafe-korafen da aka gabatar a kansu.
(NAN)
