Trends

Majalisar Dattawa ta Ƙara Wa’adin Kasafin Kuɗin Ayyukan 2025 Zuwa Satumba

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙarin wa’adin watanni uku domin aiwatar da ɓangaren manyan ayyuka na Kasafin Kuɗin 2025, inda aka matsar da wa’adin daga ranar 30 ga Yuni zuwa 30 ga Satumba, 2026.

An amince da matakin ne bayan wata buƙata da Sanata Tahir Monguno ya gabatar, da nufin hana watsi da ayyukan gwamnati tare da tabbatar da cikakken amfani da kuɗaɗen da aka riga aka saki ga Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati (MDAs).

Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa jinkirin da aka samu a harkokin saye da kwangiloli da sauran matakan gudanarwa ne suka rage saurin aiwatar da kasafin duk da cewa an saki kuɗaɗe masu yawa.

Ya ce wasu manyan ayyuka masu muhimmanci a sassa daban-daban na tattalin arziki sun kusa kammaluwa, amma suna buƙatar ƙarin lokaci domin kammala aiki, tantancewa da kuma biyan kuɗaɗen da suka dace.

Bamidele ya yi gargadin cewa idan ba a tsawaita wa’adin ba, akwai yiwuwar a yi watsi da wasu ayyuka, lamarin da zai janyo asarar albarkatu tare da kawo cikas ga shirye-shiryen gwamnati.

Bayan muhawara kan kudirin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya gabatar da shi domin amincewa ta hanyar ƙuri’ar baki, inda mafi yawan sanatoci suka goyi bayan matakin.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa ƙarin wa’adin zai taimaka wajen inganta aiwatar da kasafin kuɗi, rage almubazzaranci da tabbatar da kammala ayyukan gine-gine da sauran muhimman ayyukan raya ƙasa da ake ci gaba da gudanarwa.

Majalisar ta jaddada cewa tsawaita wa’adin ya shafi ɓangaren manyan ayyuka na Kasafin Kuɗin 2025 ne kawai, domin ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗin gwamnati da tabbatar da samun ƙima kan kuɗin jama’a.

Ana sa ran za a aika da kudurin zuwa Majalisar Wakilai domin amincewa, wanda hakan zai bai wa Ma’aikatu, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati wa’adin zuwa ranar 30 ga Satumba, 2026 domin kammala aiwatarwa, tantancewa da biyan kuɗaɗen ayyukan da ke ƙarƙashin kasafin manyan ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *