Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da daftarin sabbin ƙa’idoji da ke takaita yadda bankuna za su riƙa tallafawa ko mu’amala da kamfanonin da suke da alaƙa da su, domin hana matsalolin kuɗi da ka iya tasowa a wani kamfani su shafi sauran sassan ƙungiyar.
Sabbin ƙa’idojin na kunshe ne a cikin takardar “Exposure Draft Guidelines on Ring-Fencing Operations of Closely Linked Entities”, wadda Daraktar Sashen Manufofi da Tsare-tsaren Kuɗi ta CBN, Dakta Rita I. Sike, ta sanya wa hannu tare da miƙa wa masu ruwa da tsaki domin bayar da shawarwari.
A ƙarƙashin sabbin dokokin, duk wata mu’amala tsakanin bankuna da rassansu, ciki har da kamfanonin fasahar kuɗi (fintech), bankunan ƙananan kuɗi (microfinance), da kamfanonin holding, dole ne ta kasance bisa ƙa’idojin kasuwa, tare da cikakken rubuce-rubuce da sanar da hukumomin sa ido.
CBN ta bayyana cewa dole ne kamfanonin da ke da alaƙa da juna su gudanar da harkokinsu cikin ‘yanci, su kasance da isasshen jari da kuɗaɗen gudanarwa, sannan su ware kuɗaɗen kwastomomi daga sauran harkokin ƙungiyar.
Bankin ya yi gargadin cewa yawan dogaro da juna tsakanin irin waɗannan kamfanoni na iya sa asarar da ta faru a wani sashe ta bazu zuwa ayyukan banki da ke ƙarƙashin kulawar hukuma.
Daftarin ya kuma tanadi cewa kwamitocin gudanarwa su samar da tsare-tsaren kariya (ring-fencing policies), su takaita yawan mutanen da ke rike da mukamai a kamfanoni masu alaƙa da juna zuwa kashi 20 cikin ɗari, sannan su tabbatar da cewa duk wata mu’amalar cikin gida ana yin ta ne bisa farashin kasuwa tare da bayar da rahoto duk bayan watanni uku.
Haka kuma, duk wani rance ko garanti tsakanin kamfanonin da ke da alaƙa da juna zai bukaci amincewar hukuma kafin a aiwatar da shi.
Sabbin ƙa’idojin sun kuma wajabta samun sahalewar kwastomomi kafin a saka su cikin kayayyaki ko ayyukan wasu kamfanoni masu alaƙa, tare da bayyana musu a fili sunan kamfanin da ke bayar da sabis ɗin.
A bangaren ayyukan haɗin gwiwa, za a ƙara tsaurara sa ido ta hanyar wajabta yarjejeniyoyin matakin sabis (service-level agreements), binciken masu zaman kansu da kuma amincewar CBN.
Tsarin ya kuma mayar da hankali kan kare haƙƙin masu amfani da sabis, inda ya haramta yaudarar kwastomomi game da ayyukan da ba su cikin lasisin kamfani, tare da hana amfani da kuɗaɗen kwastomomi wajen bayar da rance ko biyan basussukan wasu kamfanonin ƙungiyar.
Haka zalika, ƙa’idojin sun wajabta bin tanade-tanaden Dokar Kare Bayanai ta Najeriya, inda aka haramta raba bayanan kwastomomi tsakanin kamfanoni masu alaƙa ba tare da izinin mai bayanan ba.
CBN ta ce duk wanda ya karya waɗannan ƙa’idoji na iya fuskantar hukunci ƙarƙashin Dokar BOFIA ta 2020, ciki har da tara, sauya shugabanni ko kuma soke lasisi.
Ana sa ran sabbin ƙa’idojin za su fara aiki daga baya a shekarar 2026 bayan kammala tuntuba da masu ruwa da tsaki, a wani ɓangare na gyare-gyaren da ake yi domin ƙarfafa gaskiya, juriya da kuma amincewar jama’a ga tsarin kuɗi na Najeriya.
