Trends

Sauye-sauyen Haraji Dole Su Kare Masu Biyan Haraji – RMAFC

Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga da Raba Su da Kula da Harkokin Kasafin Kuɗi ta Tarayya (RMAFC) ta jaddada cewa sauye-sauyen haraji da kuɗaɗen shiga da ake aiwatarwa a Najeriya dole ne su kare haƙƙin masu biyan haraji tare da tabbatar da adalci wajen rabon kuɗaɗen shiga tsakanin matakan gwamnati daban-daban.

Shugaban Hukumar, Dakta Mohammed Shehu, ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar Hukumar Haɗin Gwiwar Tara Kuɗaɗen Shiga (JRB) ta kai masa a Abuja.

Ya ce gaskiya, adalci da riƙon amana su ne ginshiƙan sauye-sauyen da ake aiwatarwa a halin yanzu.

A cewarsa, “Dole ne mu yi aiki tare domin tabbatar da cewa sauye-sauyen kuɗaɗen shiga da ake aiwatarwa suna kare muradun masu biyan haraji tare da tabbatar da adalci wajen rabon kuɗaɗen shiga.”

Shehu ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tara kuɗaɗen shiga yana da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar sauye-sauyen, yana mai ƙara da cewa daidaita manufofi da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki za su ƙarfafa bin dokokin haraji da kuma amincewar jama’a da tsarin haraji.

Ya kuma amince da cewa akwai damuwa kan batutuwan mayar da kuɗaɗen haraji (tax refunds), harajin canja wurin kuɗi ta hanyar lantarki da kuma tsarin rabon kuɗaɗen shiga, yana mai cewa ana buƙatar ci gaba da tattaunawa da musayar ra’ayoyin fasaha domin tabbatar da adalci da inganci.

A nasa jawabin, Babban Sakataren JRB, Dakta Olusegun Adesokan, ya ce manufar sauye-sauyen ita ce inganta adalci da gaskiya tare da fayyace yadda ake raba kuɗaɗen shiga tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da suka haɗa da harajin tambari (stamp duties), biyan haraji tun kafin lokacin da ya kamata da kuma harajin canja wurin kuɗi ta hanyar lantarki.

Adesokan ya ƙara da cewa an tsara sabon tsarin ne domin amfanar masu biyan haraji, hukumomin gwamnati da kuma tabbatar da daidaiton harkokin kuɗi na ƙasa, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen shiga suna komawa jihohin da suka dace.

A ƙarshen taron, bangarorin biyu sun sake jaddada aniyarsu ta kare haƙƙin masu biyan haraji, inganta tsarin tattara kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa domin tabbatar da nasarar aiwatar da sauye-sauyen.

A wani labari na daban, mutum na farko da aka naɗa a matsayin Mai Kare Haƙƙin Masu Biyan Haraji (Tax Ombud) a Najeriya, Dakta John Nwabueze, ya buƙaci ‘yan ƙasa da kamfanonin da ke fuskantar matsalolin ƙiyasin haraji marasa adalci ko kuma biyan haraji sau da yawa kan abu guda, da su nemi taimako daga sabon ofishin.

Ya bayyana cewa ofishin na samar da wata kafa mai zaman kanta domin warware rikice-rikice tsakanin masu biyan haraji da hukumomin tara kuɗaɗen shiga cikin adalci da gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *