Ƙwararrun likitocin ƙwaƙwalwa sun yi gargadin cewa maza da ke ɓoye damuwa da raɗaɗin zuciya na fuskantar haɗarin kamuwa da baƙin ciki mai tsanani, shaye-shayen ƙwayoyi, rushewar alaƙar aure ko zamantakewa, har ma da yiwuwar kisan kai.
Sun bayyana cewa al’adun al’umma da yawa na hana maza nuna raunin zuciya, lamarin da ke sa da yawa daga cikinsu su riƙa danne damuwa, baƙin ciki da fargaba a cikin zuciya har ya taru ya zama matsala mai tsanani.
A duniya baki ɗaya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa sama da mutane 720,000 ke mutuwa ta hanyar kisan kai a kowace shekara. Rahoton ya kuma nuna cewa nahiyar Afirka na da yawan mutuwar 11.5 cikin mutane 100,000, wanda ya fi matsakaicin duniya na 8.9. Haka kuma, kisan kai shi ne dalili na uku na mutuwa ga matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 29.
Da yake magana a lokacin Watan Wayar da Kai Kan Lafiyar Zuciyar Maza, Likitan Ƙwaƙwalwa mai ba da shawara, Dr Sunday Amosu, ya ce: “Al’umma na hana maza bayyana motsin zuciyarsu a fili. Idan aka dinga danne waɗannan motsin zuciyar na tsawon lokaci, haɗarin kisan kai na ƙaruwa.”
Amosu ya ce maza na mutuwa ta hanyar kisan kai sau biyu fiye da mata, kuma galibi suna amfani da hanyoyi masu haɗari. Ya ƙara da cewa alkaluman Najeriya na hukuma da ke nuna mutuwar mutane 4.4 cikin 100,000 a shekarar 2019 na iya zama ƙasa da gaskiya saboda rashin rahoto mai kyau da kuma tsoron kunyatawa.
Ya bayyana matsin tattalin arziki, shaye-shayen giya da ƙwayoyi, da kuma keɓancewa daga jama’a a matsayin manyan abubuwan da ke ƙara haɗari, yana mai cewa maza da yawa suna shan wahala a ɓoye saboda nauyin zama masu ɗaukar nauyin iyali. Ya kuma ce alamun haɗari kamar rashin fata, janyewa daga jama’a, halayen rashin kulawa da kuma shaye-shaye bai kamata a yi watsi da su ba.
Wani likitan ƙwaƙwalwa daga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH), Dr Kehinde Oderinde, ya ce tsoron a yi wa mutum kallon mahaukaci yana hana mutane da yawa neman taimako. Ya ce: “Mutane na tsoron a yi musu hukunci ko a yi musu lakabi da ‘mahaukata’. Wannan tsoro yana hana su neman taimakon da suke bukata.”
Dukkanin ƙwararrun sun yi kira ga maza da su nemi taimakon ƙwararru da wuri, yayin da iyalai da al’umma su riƙa nuna tausayi maimakon suka. Sun jaddada cewa ƙara wayar da kai, gano matsala da wuri, da samar da yanayin da ke goyon bayan lafiyar hankali na da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗarin kisan kai a tsakanin maza.
