Ƙungiyar Magunguna ta Najeriya (PSN) ta bayyana cewa ƙasar na fuskantar barazana mai tsanani ga lafiyar jama’a, inda ta ce akwai kimanin kantunan sayar da magunguna na bogi miliyan uku a faɗin ƙasar, idan aka kwatanta da ƙasa da 50,000 da aka yi wa rajista a hukumance.
Shugaban PSN, Ayuba Tanko, ya ce yawaitar waɗannan kantuna da ba su da rajista na jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin haɗarin amfani da magunguna marasa inganci tare da karɓar magani daga mutane marasa ƙwarewa. Ya kuma yaba wa hukunce-hukuncen Kotun Tarayya da suka yanke wa masu gudanar da irin waɗannan kantuna hukuncin ɗaurin kurkuku a Ibadan da Calabar, yana mai cewa hakan mataki ne na kare lafiyar jama’a.
Tanko ya ce matsalar ta samo asali ne tun lokacin da aka damƙa bayar da lasisin masu sayar da magungunan Patent and Proprietary Medicine Vendors (PPMVL) ga ƙananan hukumomi, abin da ya haifar da hukumomi 774 na bayar da lasisi tare da ƙara yawaitar kantuna ba tare da kulawa ba.
Ya ce: “Harkokin magunguna suna cikin jerin dokokin da ke ƙarƙashin ikon majalisar tarayya saboda muhimmancinsu. A fannin lafiya, aikin likitancin magunguna shi ne kaɗai da ke da alaƙa kai tsaye da wannan jerin saboda muhimmancin sarrafa magunguna.”
PSN ta yaba wa Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) bisa ƙara tsaurara matakan sa ido, inda ta jaddada cewa duk wani kantin magani dole ne ya kasance ƙarƙashin kulawar ƙwararren Pharmacist kamar yadda dokar PCN ta 2022 ta tanada. Waɗannan ƙwararru ne ke sa ido kan saye, adanawa, bayar da magunguna da kuma ba marasa lafiya shawarwari.
Tanko ya yi gargadin cewa barin mutane marasa ƙwarewa su riƙa adana da bayar da magunguna a asibitoci da wurare masu zaman kansu na rage ingancin kulawar lafiya a ƙasar. Ya kuma yi kira da a yi gyaran dokar Fake Drug Act, yana mai cewa raunin hukunci na ƙara ƙarfafa masu karya doka.
Ya ce: “Duk wanda ya karya dokar PCN Act 2022 da kuma sashe na 2 na Fake Drug Act dole ne ya fuskanci hukunci. Dole ne a ƙara tsaurara aiwatar da doka da hukunci mai tsanani domin kare ’yan Najeriya daga magunguna marasa inganci.”
Ƙungiyar PSN ta ƙara jaddada cewa ƙarfafa dokoki, tsaurara hukunci, da ingantaccen sa ido suna da matuƙar muhimmanci wajen kare tsarin rarraba magunguna a Najeriya da kuma dawo da amincewar jama’a ga tsarin kiwon lafiya.
